Zaɓen ƙananan hukumomi yana nan ba fashi —Majalisar Kano

Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta ce babu gudu babu ja da baya a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe ranar Asabar.

Zaɓen ƙananan hukumomi yana nan ba fashi —Majalisar Kano

Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta ce babu gudu babu ja da baya a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe ranar Asabar.

Majalisar ta jaddada babu abin da zai hana gudanar da zaben ƙananan hukumomi kamar yadda aka tsara a ranar Asabar 26 ga watan Oktoba, 2024.

Wannan mataki na zuwa ne bayan umarnin Babbar Kotun Tarayya na bayar na hana Hukumar Zaɓe ta Jihar Kano (KANSIEC) gudanar da zaɓen.

Mai shari’a Simon Amobeda ya ba da umarnin ne tare rushe shugabancin hukumar zaɓen bisa dogaro da hujjojin da aka gabatar na rashin cancantar shugabannin.

Sai dai shugaban masu rinjaye a majalisar, Lawan Hussaini Dala ya ce za su gudanar da zaɓen wanda dama tuni sun tanadi matakan da za a bi don ganin zaɓen ya gudana kamar yadda aka tsara