Zaɓen ƙananan hukumomin Osun na nan daram – Gwamna Adeleke
Gwamnan ya ce mutanen jihar a shirye suke tsaf kuma babu gudu babu ja da baya kan gudanar da zaɓen.

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke ya ce ya sha alwashin cewa zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi a jihar a gobe Asabar zai gudana kamar yadda aka tsara.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a matsayin martani kan shawarar da ministan shari’a na Najeriya, Lateef Fagbemi, wanda ya buƙaci gwamnatin jihar ta dakatar da yunƙurin yin sabon zaɓen ƙananan hukumomi.
- Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter Obi
- An ƙwace miliyoyin daloli, gidajen da ke da alaƙa da Emefiele
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, Ministan ya ce kotu ta dawo da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin da aka zaɓa a ƙarƙashin tsohon Gwamna Gboyega Oyetola, amma ta tsige su ta hanyar umarnin zartarwa da gwamnan ya yi.
Fagbemi ya ce ba bisa ƙa’ida ba ne a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Osun kafin watan Oktoba lokacin da wa’adin shugabanni da kansilolin da aka zaɓa a Jam’iyyar APC zai ƙare.
Sai dai a wata sanarwa da kakakin Gwamnan, Olawale Rasheed ya fitar, gwamnan ya ce mutanen jihar a shirye suke tsaf kuma babu gudu babu ja da baya kan gudanar da zaɓen.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake karɓar rukunin gamayyar ƙungiyoyin farar hula da suka je jihar domin sanya ido kan zaɓen ƙananan hukumomi.