Zaɓen Edo: Abin da ya kai ni Ofishin INEC — Obaseki
APC ta ce ziyarar da Gwamna Obaseki ya kai Ofishin INEC ɗin wuce gona da iri ne.
Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya bayyana dalilin da ya kai shi ofishin Hukumar Zaɓe ta INEC, inda ake tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.
Aminiya ta ruwaito yadda Mataimakin Babban Sufeton ’Yan sanda, Frank Mba da ke sa ido kan zaɓen, tare da tawagar jami’ansa suka fitar da Gwamna Obaseki daga ofishin na INEC da Asubahin yau Lahadi.
- An kama matan da suka yi yunƙurin sayar da tagwayen jarirai a Legas
- Mazauna gaɓar Kogin Benuwe sun soma ƙaurace wa gidajensu
Gwamna Obaseki wanda ya isa cibiyar tattara sakamakon zaɓen da misalin ƙarfe 3:00 na dare, ya yi wata ganawar sirri da Kwamishinan Zaɓen a ofishinsa.
Sai dai yayin da wannan ganawa ke gudana, wasu ’yan jam’iyyar adawa ta APC suka soma tayar da jijiyoyin wuya da cewa gwamnan ya wuce gona da iri saboda abin da suka bayyana cewa ba shi da wani hurumi a ofishin na INEC.
Daga cikin waɗanda suka yi adawa da ziyarar gwamnan har da Sakataren APC na ƙasa, Ajibola Basiru da kuma ɗan takarar kujerar Mataimakin Gwamna na APC, Dennis Idahosa.
Sai dai da yake yi wa manema labarai ƙarin haske daga Cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke birnin Benin, Gwamna Obaseki ya ce ya ziyarci ofishin ne bayan samun labarin cewa Hukumar INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaɓen.
“Da misalin ƙarfe 1:00 na dare na samu labarin cewa za a mayar da cibiyar tattara sakamakon zaɓen zuwa Babban Hedikwatar INEC.
“Sannan kuma na samu labarin cewa an hana wasu daga cikin wakilan jam’iyyarmu ta PDP shiga cibiyar tattara sakamakon zaɓen.
“Saboda haka a daidai wannan lokaci ne na kira Babban Kwamishinan Zaɓen domin jin bahasi kan lamarin amma bai amsa wayarsa ba.
“Wannan dalilin ya sanya na kai ziyara ofishin inda na gana da Kwamishinan Zaɓen kan tsare-tsaren da suka tanada dangane da tattara sakamakon zaɓen.”