Zaɓen Edo: Ana ci gaba da ƙirga ƙuri’u
Rahotanni sun bayyana cewar an kammala kaɗa ƙuri’u, yanzu haka an fara ƙirga sakamakon zaɓen a matakin ƙananan hukumomi.
An rufe rumfunan zaɓe bayan kammala kaɗa ƙuri’u a zaɓen Gwamnan Jihar Edo da aka gudanar ranar Asabar.
Tuni aka fara ƙirga ƙuri’u a matakin rumfunan zaɓen.
- Zaɓen Edo: INEC ta tsawaita kaɗa ƙuri’a a wasu yankuna
- Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda
Rahotonni sun nuna cewar an gudanar da zaɓen ba tare da matsala a wurare da dama a faɗin jihar.
A yanzu hankula sun fara karkata kan cibiyoyin tattara sakamakon zaɓen, domin tattara sakamakon a matakin ƙaramar hukuma kafin daga bisani a tafi matakin jiha.
Manyan jam’iyyun siyasar jihar guda uku; PDP, APC da kuma LP na son ganin ɗan takararta ya lashe zaɓen jihar.