Zaɓen Edo: APC ta buƙaci a tsige Obaseki saboda kalaman tayar da rikici

Idan ba a gudanar da zaɓe na gaskiya a Edo ba, hakan zai iya haifar da rikici a Nijeriya.

Zaɓen Edo: APC ta buƙaci a tsige Obaseki saboda kalaman tayar da rikici

Gwamnan Edo Godwin Obaseki

Jam’iyyar APC reshen Jihar Edo, ta yi kira ga Majalisar Dokokin Jihar ta fara shirin tsige Gwamna Godwin Obaseki, bisa zarginsa da yin kalaman da suke barazana ga ƙasar nan.

Shugaban riƙo na Jam’iyyar APC a jihar Mista Jarret Tenebe ne ya yi wannan kira a wata sanarwa da ya fitar.

Jam’iyyar APC ta yi wannan kira ne bayan wani bidiyo da aka ga Gwamna Obaseki na barazarar zai ƙona Nijeriya, idan ba a kama waɗanda suka hallaka Sufeton ’yan sanda Akor Onuh a filin jirgin sama na Benin ba.

Bayanai sun ce al’umma da dama a kafofin sadarwar zamani na ta yabon Gwamna Godwin Obaseki a kan waɗannan kalamai nasa da suka kasance barazana ga zaman lafiyar ƙasa.

Don tabbatar da ganin an daƙile tare da kawo ƙarshen irin waɗannan munanan kalamai da tsare-tsare da ake zargin Gwamnan na yi, Jam’iyyar APC ta buƙaci ’yan Majalisar Dokokin Jihar Edo su gaggauta fara shirin tsige shi.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa Gwamna Obaseki ya bai wa Ƙungiyar Tsaro ta Jihar Edo (ESSN) da kuma ’yan sa-kai (PUWOƁ) makamai domin kashewa da kuma raunata duk wanda ya saɓa ra’ayin gwamnatinsa.

Da yake mayar da martani, Gwamna Obaseki ta bakin Kwamishinan Sadarwa da Wayar da kan Jama’a, Mista Chris Nehikhare, ya musanta zargin, yana mai cewa Jam’iyyar APC na ƙoƙarin canza kalaman Gwamnan ne.

Mista Nehikhare ya ce Gwamnan ya yi taro da masu ruwa-da-tsaki a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce, “Idan ba a bar zaɓe na gaskiya da adalci ya gudana a Jihar Edo a ranar 21 ga Satumba ba, to hakan zai iya haifar da babban rikici a Nijeriya.”