Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda

Waɗanda aka sahalewa ne kaɗai ne ke damar zirga-zirga a ranar zaɓe.

Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda

Mataimakin Babban Sufeton ’Yan sanda, Frank Mba

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta buƙaci duk wanda ya kaɗa ƙuri’arsa a Zaɓen Gwamnan Edo da ke gudana yanzu haka da ya koma gida ya zauna.

Mataimakin Babban Sufeton ’Yan sanda, Frank Mba ne ya bayyana hakan yayin wata hira ta musamman da gidan talabijin na Channels dangane da zaɓen.

Aminiya ta ruwaito cewa wasu jagororin ’yan siyasa sun umarci masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen da su tabbatar sun tsaya sun kare ƙuri’unsu domin ganin cewa ba a yi musu maguɗi ba.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar yayin gabatar da jawabai a birnin Benin, ya shawarci masu kaɗa ƙuri’a da su tabbatar sun tsaya sun kare haƙƙinsu a yayin zaɓen na yau Asabar.

“Ba zai yiwu a zo Edo a yi satar ƙuri’u ba. Saboda haka ku tabbatar kun fita kun yi zaɓe sannan ku tsaya ku tsare ƙuri’unku.

“Ku raka ƙuri’unku sannan ku tabbatar kun tsaya an sanar da sakamako. Idan kun yi wannan babu wanda zai sauya sakamakon ƙuri’un da kuka kaɗa,” a cewar Atiku.

Sai dai Mista Mba ya ce dole ne duk wanda ya kaɗa ƙuri’arsa ya koma gida ya zauna, yana mai cewa waɗanda aka sahalewa ne kaɗai ne ke damar yin wata zirga-zirga.

“Yana da muhimmanci iyaye da sauran al’umma su fahimci cewa duk waɗanda ba a bai wa dama ba, ba su da damar gudanar da duk zirga-zirga a ranar zaɓe.

“Abin da kawai jama’a za su yi shi ne su fita su yi zaɓe kamar yadda doka ta ba su ’yanci sannan su koma gida su zauna,” a cewar Mba.

Shi ma Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Olukayode Egbetokun, ya ba da umarnin taƙaita zirga-zirga a jihar ta Edo.

Babban sufeton ‘yan sandan ya ce an yi haka ne domin tabbatar da cewa an ɗauki matakan da suka dace wajen gudanar da sahihin zabe cikin gaskiya da lumana.

A sanarwar da ya fitar jiya Juma’a, kakakin rundunar ‘yan sandan, Muyiwa Adejobi ya ce babban sufeton ya ba da umarnin taƙaita zirga-zirgar ababen hawa akan tituna da hanyoyin ruwa da dukkanin nau’ukan harkokin sufuri tun daga karfe 6 na safe har zuwa 6 na yamma a ranar zaɓen.

Ya kuma kara da cewa waɗanda umarnin ya tsame sun haɗa da, kafafen yaɗa labaran da aka tantance da jami’an zabe da motocin ɗaukar marasa lafiya da kuma ma’aikatan ba da agajin gaggawa.

Aƙalla ’yan takara da jam’iyyun siyasa 17 ne ke fafatawa a zaɓen da suka haɗa da maza 16 da mace ɗaya, inda manyan jam’iyyun suka kasance APC da PDP da kuma jam’iyyar Labour.

DAGA LARABA: Yadda sunayen zamani suka shafe na Hausawa

Sojoji da dama sun ɓace bayan harin Boko Haram a Borno

NFF ta naɗa Éric Chelle a matsayin sabon kocin Super Eagles

Abba ya nemi Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin Hajjin 2025