Zaɓen Edo: INEC ta tsawaita kaɗa ƙuri’a a wasu yankuna

INEC ta ce ta tsawaita lokacin ne don tabbatar da cewa kowa ya samu damar kaɗa ƙuri’arsa.

Zaɓen Edo: INEC ta tsawaita kaɗa ƙuri’a a wasu yankuna

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tsawaita lokacin kaɗa ƙuri’a a yankunan da aka fara zaɓe a makare.

Aminiya ta ruwaito yadda aka samu jinkiri a wasu sassan jihar sakamakon ruwan sama da kuma wasu matsaloli da suka shafi raba kayan zaɓe.

Jami’an INEC da kayan zaɓe sun isa wasu yankuna a makare, kamar rumfar zaɓe ta uku a Ewohimi,da ke ƙaramar hukumar Esan ta Arewa, inda ɗan takarar jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo, ya yi kaɗa ƙuri’arsa.

Ighodalo, wanda ya isa wajen zaɓe da misalin ƙarfe 10:30 na safe, ya koka kan jinkirin isowar kayan zaɓe a ƙaramar hukumar Owan ta Yamma.

“Kamar yadda kuke gani, jami’an INEC da kayan zaɓe sun iso yanzu, kuma sun makara sama da sa’o’i biyu,” in ji shi.

“Duk da haka, har yanzu ana kan aikin tantance mu don yin zaɓe, bari mu ga abin da za mu iya yi kafin lokacin da aka ware.”

Ya ƙara da cewa, tsawaita lokacin zaɓen zai taimaka wajen yi wa kowa adalci.

Kwamishinan INEC na ƙasa, Mohammed Haruna ne, ya sanar da cewa za a tsawaita zaɓe a yankunan da abin ya shafa.

Ya ce, “Hukumar na ci gaba da sanya ido kan zaɓen gwamna na Jihar Edo daga ɗakinmu na sanya ido da ke hedikwatar Abuja. Mun lura cewa an fara zaɓe da wuri a yawancin rumfunan zaɓen jihar, amma an samu rahotannin samun jinkiri a wasu wurare.

“Don tabbatar da cewa ba a hana kowa yin zaɓe ba, hukumar tana tabbatar da cewa, bisa ƙa’idojinmu, za a tsawaita lokacin zaɓe a wuraren da aka fara a makare, kuma zaɓe zai ci gaba da gudana har zuwa ƙarfe 2:30 na rana.

“Haka kuma, mun sanar da ofishinmu na Jihar Edo don tabbatar da cewa, a tabbatar akwai wutar lantarki da janareto a rumfunan zaɓe ko cibiyoyin tattara sakamako da abin ya shafa.”