Zaɓen Edo: Magoya bayan PDP sun fara zanga-zanga
Yanzu haka dai ana dakon sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi biyu da suka rage.
Magoya bayan Jam’iyyar PDP, sun fara zanga-zanga yayin da ake dakon sakamakon ƙananan hukumomi biyu da suka rage a Zaɓen Gwamnan Jihar Edo.
Jam’iyyar APC, wadda ita ce babbar jam’iyyar adawa a Edo, tana kan gaba a zaɓen bisa sakamakon da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana.
- Tsadar Rayuwa: Matar Tinubu ta raba wa ɗalibai littafan rubutu a Nasawara
- An kama matan da suka yi yunƙurin sayar da tagwayen jarirai a Legas
Magoya bayan PDP, sun mamaye hedikwatar INEC da ke birnin Benin, don yin zanga-zanga kan sakamakon zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar, wanda har yanzu ake ci gaba da ƙirga ƙuri’u.
INEC, ta dakatar da bayyana sakamakon bayan ta bayyana sakamakon ƙananan hukumomi 16 daga cikin 18 da ke jihar.
A halin yanzu, APC ta yi nasara a ƙananan hukumomi 10, yayin da PDP ta yi nasara a ƙananan hukumomi guda shida.
Ana sa ran INEC za ta sanar da sakamakon sauran ƙananan hukumomi biyu da suka rage a yammacin ranar Lahadi.
Tun da farko Aminiya, ta ruwaito yadda APC ta kasance a kan gaba da ƙuri’u 244,549, sai PDP da ƙuri’u 195,954, yayin da jam’iyyar LP ke da ƙuri’u 13,348.