Zaɓen Edo: Yadda aka kama masu sayen ƙuri’a da ’yan daba

Rundunar ta ce za ta tabbatar zaɓen ya kammalu cikin lumana.

Zaɓen Edo: Yadda aka kama masu sayen ƙuri’a da ’yan daba

Jami’an ’Yan Sandan Najeriya, sun kama wasu da ake zargi da siyan ƙuri’a a zaɓen gwamna da ya gudana a ranar Asabar a Jihar Edo.

Har wa yau, jami’an sun kama wasu ’yan daba ake kyautata zaton magoya bayan jam’iyyar PDP ne.

A cewar sanarwar kakakin rundunar ’yan sandan, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce sun kama su ne bayan wani shiri da aka yi na kai samame a wasu wurare.

An kama mutum biyu, Emotingham Godspower, mai shekara 25 da Farawei Isaac, mai shekara 27, kuma dukkaninsu sun fito ne daga yankin Ufunama da ke ƙaramar hukumar Ovia ta Kudu Maso Yamma a Jihar Edo.

An kama mutanen ne a gidan So Cash Guest House da ke Ekpoma, inda aka samu kuɗi da wasu kayan da suka saɓa doka.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an kama wasu mutum shida a makarantar sakandare ta Aibotse da ke yankin Auchi kan sayen ƙuri’u.

Adejobi ya ce, “Shirin da jami’anmu suka tsara cikin hikima ya daƙile ƙoƙarin waɗanda ke son lalata tsarin zaɓen. Mun ƙuduri aniyar tabbatar an kammala zaɓen mai cikin lumana.”

Ya ce rundunar na ci gaba da gudanar da bincike, kuma za ta riƙe fitar da bayanai yayin da abubuwa ke faruwa dangane da zaɓen.

Zaɓen Edo: Yadda aka kama masu sayen ƙuri’a da ’yan daba

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina