Zaɓen Edo: ’Yan sanda sun fitar da Gwamna Obaseki daga ofishin INEC

INEC ta sanar da cewa za a soma tattara sakamakon zaɓen da misalin ƙarfe 10:00 na wannan safiyar.

Zaɓen Edo: ’Yan sanda sun fitar da Gwamna Obaseki daga ofishin INEC

Mataimakin Babban Sufeton ’Yan sanda, Frank Mba da ke sa ido kan Zaɓen Edo, ya bai wa jami’ansa umarnin fitar da Gwamna Godwin Obaseki daga ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC da ke jihar.

Tun farko dai an samu jinkirin soma tattara sakamakon zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar, inda Hukumar INEC ta alaƙanta hakan da ruwan sama da ya riƙa sauka tun ana kaɗa ƙuri’ar.

Wannan jinkiri na fara tattara sakamakon ne ya sanya Gwamna Obaseki a fusace ya kai ziyara Ofishin INEC tare da tawagar wasu hadimansa da misalin ƙarfe 3:00 na dare.

Kai tsaye gwamnan ya wuce Ofishin Babban Kwamishinan Zaɓen na INEC inda suka yi wata ganawar sirri.

Sai dai wannan lamari bai yi wa wasu magoya bayan jam’iyyar APC daɗi ba, inda suka riƙa bubbuga ƙofar shiga ofishin suna karatsin cewa Gwamnan ba shi da hurumi domin shi ba jami’in INEC ba ne.

Wasu daga cikin masu wannan adawa sun haɗa da Sakataren APC na ƙasa, Ajibola Basiru da kuma ɗan takarar kujerar Mataimakin Gwamna na APC, Dennis Idahosa.

A cewar Idahosa, “Dole Obaseki ya fito saboda bai kamata ya kasance a nan [Ofishin INEC] ba. Ba ma’aikacin INEC ba ne saboda haka kada ’yan sanda su bari a yi wa lamarin ƙafar ungulu.”

Da yake zantawa da manema labarai, Sakataren APC na ƙasa, Surajudeen Basiru, ya bayyana abin da Gwamna Obaseki ya yi a matsayin wuce gona da iri.

A cewar Basiru, “Obaseki ba ɗan takara ba ne a wannan zaɓen saboda haka ba shi da hurumin zuwa Ofishin INEC a wannan lokaci. Wannan ai wuce gona da iri ne.”

Aminiya ta ruwaito cewa a yayin da wannan lamari ya riƙa yamutsa hazo da janyo ta da jijiyoyin wuya, Mataimakin Babban Sufeton ’Yan sanda Frank Mba ya shiga ofishin na INEC, inda ya bai wa gwamnan umarnin ya san inda dare ya yi masa.

Sai dai jim kaɗan bayan faruwar wannan lamari, INEC ta sanar da cewa za a soma tattara sakamakon zaɓen da misalin ƙarfe 10:00 na wannan safiyar.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos