Zaɓen Edo: Za mu kare ƙuri’unmu da jininmu — PDP

Shugaban ya ce PDP ba za ta yarda a sanar da sakamakon zaɓen cikin dare ba.

Zaɓen Edo: Za mu kare ƙuri’unmu da jininmu — PDP

Shugaban Riƙo na Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Illiya Damagum, ya ce za su kare ƙuri’unsu da rayukansu a zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Edo ranar 21 ga watan Satumba.

Ya gargaɗi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) da kada ta sanar da sakamakon zaɓen da cikin dare.

Damagum, ya yi wannan jawabi ne a lokacin taron ƙarshe na yaƙin neman zaɓen PDP a Edo.

A yayin taron ya miƙa tutar jam’iyyar ga ɗan takarar gwamna na jihar, Dokta Asue Ighodalo.

Ya jaddada cewa jam’iyyar PDP za ta kasance a ankare don hana sanar da sakamako da daddare.

Ya zargi jam’iyyar adawa da shirya yin maguɗin zaɓe, amma ya yi alƙawarin cewa PDP za ta tsaya tsayin-daka don kare ƙuri’unsu.

Damagum, ya kuma yi kira ga magoya bayan PDP da su fito ƙwansu da kwarkwatarsu su jefa ƙuri’a tare da kare ƙuri’unsu.

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, wanda shi ne shugaban kwamitin kamfen na PDP na ƙasa, ya gargaɗi duk wani yunƙuri na yin maguɗi a lokacin zaɓen.

Ya nuna ƙwarin gwiwar cewa ba za a yi wa PDP maguɗk ba, sannan ya yi kira ga mutanen Edo su zaɓi Ighodalo a matsayin wanda zai gaji gwamna Obaseki.

Ɗan takarar jam’iyyar, Doka Ighodalo, ya ce Gwamna Obaseki ya gina harsashen ci gaba a jihar, kuma idan aka zaɓe shi, zai ci gaba daga inda ya tsaya.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya buƙaci masu zaɓe da su kare ƙuri’unsu kuma su tabbatar da an sanar da sakamakon daidai.

Ya yi alƙawarin cewa idan suka yi hakan, PDP za ta lashe zaɓen ranar 21 ga Satumba.

Shugabanni da dama sun halarci taron, ciki har da gwamnonin PDP, Sanata Aba Moro, Cif Tom Ikimi, mambobin Majalisar Jihar, da mambobin Majalisar Wakilai.

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra