Zaɓen Gwamna: APC ta kama hanyar lashe zaɓen Edo

Ya zuwa yanzu dai APC ta bai wa jami’yyar PDP tazarar ƙuri’u 79,375.

Zaɓen Gwamna: APC ta kama hanyar lashe zaɓen Edo

Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamna da aka gudanar a Jihar Edo ranar Asabar, Sanata Monday Okpebholo na gab da lashe zaɓen.

Ɗan takarar jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo ne, ke biye masa a baya, yayin da Olumide Akpata na jam’iyyar LP ke matsayi na uku.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta fitar da sakamakon ƙananan hukumomi 17 ya zuwa yanzu.

Aminiya ta ruwaito cewar ɗan takarar APC, ya yi nasara a ƙananan hukumomi 11 daga cikin 16 da aka tattara sakamakonsu.

Okpebholo, ya samu ƙuri’u 275,329, yayin da Ighodalo ya samu ƙuri’u 195,954, wanda akwai tazarar ƙuri’u 79,375 a tsakaninsu.

Sakamakon ƙaramar hukumar Ikpoba-Okha ne kaɗai ake dakonsa.

Sai dai jam’iyyar PDP mai mulkim jihar ta yi watsi da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin da APC ta lashe.

Wakilin jam’iyyar, Osagbovo Iyoha, wanda shi ne Shugaban Ma’aikatan Gwamnan Jihar Edo, ya zargi INEC da canja sakamakon zaɓen.

Ya ce jam’iyyar ta yi watsi da sakamakon saboda bai wakilci ra’ayin mutanen Edo ba.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara