Zaɓen Kano: Ranar Litinin Kotun Daukaka Kara Za Ta Saurari Karar Abba
Gwamna Abba na kalubalantar soke nasarar zabensa da kotun zaben gwamna ta yi
Kotun Daukaka Kara za ta yi zama a ranar Litinin kan karar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya daukaka kan soke zaɓensa.
Kotun ta sanya ranar ne bayan Gwamna Abba na Jam’iyyar NNPP ya bayyana a matsayin rashin adalci, hukuncin da kotun farko ta yanke na ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.
A ranar 20 ga watan Satumba, 2023, alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano karkashin jagorancin mai shari Mai Shari’a Oluyemi Akintan Osadebay suka soke nasarar Abba, bayan sun soke 165,663 daga cikin kuri’un da ya samu a matsayin ba halastattu ba.
Alkalan sun soke kuri’un ne bisa hujjar rashin kwanan wata da kuma rashin hatimin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a jikin takardun kuri’un, abin da Gwamna Abba ya kira “rashin adalci” da kuma yi wa “tsarin shari’a dibar karan mahaukaciya.”
A kan haka ne ya yi alkawarin daukaka kara tare da bayyana kwarin gwiwar zai samu adalci a kotun gaba.
A ranar 18 ga watan Maris INEC ta ayyana Abba a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da kuri’u 1,019,602 a yayin da Gawuna ya zo na biyu da kuri’u 890,705.
Amma bayan soke 165,663 daga kuri’un da Abba ya samu, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan ta bayyana bayyana cewa kuri’unsa sun koma 853, 939, a yayin da Gawuna mai kuri’u 890,705 ya sha gabansa.
Hakazalika kotun ta ayyana Gawuna a halastaccen zabebben Gwamnan Jihar Kano, ta umarci INEC ta ba shi takardar shaidar cin zabe, ta kuma soke na Abba.