Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu
Ɗan takarar na PDP ya ce bai gamsu da sakamakon zaɓen Gwamnan Jihar da INEC ta ayyana ba.
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Ondo, Agboola Ajayi, ya yi watsi da sakamakon zaɓen da aka gudanar, inda ya ce zai ƙalubalanci sakamakon a kotu.
Lucky Aiyedatiwa na jam’iyyar APC, aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 366,781, yayin da Ajayi ya samu ƙuri’u 117,845.
- Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi
- Mutum 25 sun rasu bayan bullar sabuwar Annoba a Sakkwato
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ayo Fadaka, ya fitar, Ajayi ya ce zai tafi kotu domin ƙalubalantar rashin adalci a zaɓen.
“Mun yi watsi da sakamakon zaɓen ranar 16 ga watan Nuwamba, kuma za mu ɗauki matakin shari’a don gyara wannan rashin adalci.
“Muna da yaƙinin cewa Allah da kuma al’umma za su yi mana adalci. Lokaci ya yi da za a daina aikata laifuka a tsarin zaɓenmu,” in ji shi.
Ajayi ya zargi INEC da yin katsa-landan a zaɓukan bayan tun bayan hawan APC mulki a 2015.
Ya ce, “Mun gano wasu matakan da aka ɗauka don dagula zaɓen al’umma a wannan zaɓen. Dimokuraɗiyya ba za ta samu ci gaba ba idan zaɓuka suna tafiya bisa maguɗi da katsa-landan daga hukumar da ke da alhakin kare muradun masu zaɓe da tabbatar da adalci.”
Ajayi ya kuma ce INEC ta ci gaba da yin maguɗi a zaɓuka, wanda hakan ke rage wa jama’a sha’awar fita zaɓe da kuma haifar da rashin amincewa ga tsarin zaɓe gaba ɗaya.