Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Atiku ya ce jam’iyyar PDP ta za ta lamunci maguɗin zaɓe daga hukumar INEC ba.

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci ‘ya’yan jam’iyyar PDP a Jihar Ondo, su haɗa kai don samun nasara a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a ranar Asabar.

A wata sanarwa daga mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, Atiku ya yaba wa ɗan takarar PDP, Agboola Ajayi, a matsayin gogaggen ɗan siyasa wanda zai iya jagorantar jam’iyyar zuwa ga nasara da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar.

Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya kuma gargaɗi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), da sauran jami’ai da su daƙile duk wani maguɗin zaɓe.

Ya ce, “Wannan zaɓen gwamnan da zai gudana a ranar Asabar wata dama ce ga al’ummar Jihar Ondo da za su inganta ci gaban jihar.”

Ya ƙara da cewa jam’iyyar APC, wadda ke mulki yanzu, ba ta da farin jini kuma ba ta damu da buƙatun al’umma ba.

A cewarsa, Ajayi na jami’yyar PDP zai bai wa masu zaɓe mamaki ta hanyar nuna cewa mutanen jihar sun gaji da APC.

Atiku, ya tabbatar da cewa shugabannin PDP za su bayar da dukkanin goyon bayan da ake buƙata domin tabbatar da cewa APC ba ta hana mutane zaɓar abin da suke so ba a wannan zaɓen.

Ya kuma gargaɗi jami’an zaɓe da cewa PDP za ta tsaya kai da fata wajen ƙin yarda da duk wani maguɗi.

Har ila yau, Atiku ya buƙaci al’ummar Jihar Ondo, da su fito ƙwansu da kwarkwata don kaɗa ƙuri’a kuma su tabbatar an ƙirga ƙuri’unsu.