Zaɓen Ondo: Wanda bai gamsu ba ya garzaya kotu — Tinubu

Tinubu ya ce duk wanda bai gamsu da sakamakon zaɓen ba ya garzaya kotu domin neman haƙƙinsa.

Zaɓen Ondo: Wanda bai gamsu ba ya garzaya kotu — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu, ya shawarci ‘yan takarar da ba su gamsu da sakamakon zaɓen Gwamnan Jihar Ondo ba, da su garzaya kotu domin neman haƙƙinsu.

Shugaban, ya taya Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam’iyyar APC murnar lashe zaɓen.

Har ila yau, ya jinjina wa sauran ‘yan takara daga jam’iyyu 17 kan kishin ƙasa da dattako da suka nuna a lokacin yaƙin neman zaɓe da kuma lokacin zaɓen, inda ta ce hakan ya taimaka wajen samun nasarar zaɓen.

Mai bai wa Shugaban Shawara kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

“Duk wanda bai gamsu da sakamakon zaɓen ba zai iya bin hanyar shari’a don neman adalci,” in ji Onanuga.

Shugaba Tinubu ya bayyana zaɓen Jihar Ondo a matsayin gwajin dafi ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), inda ta ce ta shirya sahihin zaɓe.

Ya kuma yaba wa INEC kan ɗora kashi 98 na sakamakon zaɓen na’urar zaɓe.

Shugaban ya gode wa hukumomin tsaro, ciki har da ‘yan sanda, Sibil Difes, Hukumar Kiyaye Haɗura (FRSC), NYSC, sojoji, da sauran hukumomin tsaro, kan rawar da suka taka wajen tabbatar da zaman lafiya yayin zaɓen.

Tinubu zai halarci taron G20 a Brazil

Zaɓen Ondo: Wanda bai gamsu ba ya garzaya kotu — Tinubu

Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaɓen Gwamnan Ondo

Ba na yi wa Tinubu hassada — Atiku