Zaɓen Shugaban Ƙasa ya ɗauki harama a Senegal

Zaɓen shugaban ƙasar na yanzu shi ne na biyar tun bayan samun ’yancin kai da Senegal ta yi a 1960.

Zaɓen Shugaban Ƙasa ya ɗauki harama a Senegal

Dubban jama’a ne suke fito domin sauke nauyin da ke wuyansu na zaɓen shugaban kasa da na ’yan majalisar dokoki a Senegal.

Wannan dai na zuwa ne bayan dambarwar siyasar da ta mamaye kasar har ma da batun rashin tabbas kan makomar siyasar kasar.

Zaɓen shugaban ƙasar na yanzu shi ne na biyar tun bayan samun ’yancin kai da Senegal ta yi a 1960.

Kimanin mutane milyan 7.3 ne suka yi rajistar kada kuri’a a kasar ta Senegal da ke Yammacin Afirka.

Za a iya cewa an samu ƙarin yawan masu zaɓe a wannan karon idan aka kwatanta da 2019 lokacin da mutum miliyan 6.6 suka yi zaɓe.

Kamar yadda dokar kasar ta tanadar, za a rufe rumfunan zaɓe da misalin karfe 6 na yamma agogon GMT, inda za a sanar da sakamakon zaben a cikin mako mai zuwa.

Idan babu ɗan takarar da ya samu wannan nasara sai a sake komawa zagaye na biyu tsakanin waɗanda suka fi samun rinjaye, makonni biyu bayan sanar da zaɓen farko.

Daruruwan masu sa ido ne suka isa Senegal, kasar da ke riƙe da kambun gudanar da sahihin zaɓe da kuma bunkasar dimokuraɗiyya a yankin ƙasashen Yammacin Afirka.

Rahotannin sun tabbatar da isar masu sa ido daga ƙungiyoyin fararen hula da ƙungiyar raya kasashen Afirka ta AU da ƙungiyar bunkasa ci gaban tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS har ma da wakilcin ƙungiyar Tarayyar Turai EU.

Dukkan ’yan takarar da suke shiga zaɓen sun yi hasashen samun nasara a zagayen farko kama daga ɗan takarar da ke samun goyon bayan shugaban kasar mai barin gado Macky Sall wato Amadou Ba, da ɗan takarar da ke samun goyon bayan Karim Wade da aka haramta masa takara wato Bassirou Diomaye Faye harma da tsohon magajin garin birnin Dakar, Khalifa Sall.