Zaɓin Ganduje lalata tsarin APC ne – Salihu Lukman
Daga Saawuaa Terzunge Mataimakin shugaban APC shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya ce maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje kamar kashe jam’iyyar ne. A ranar Laraba ne dai ƙusoshin APC suka tabbatar wa da Aminiya cewa shugaba Tinubu zai damƙa shugabancin jam’iyyar a hannun Ganduje. Sai dai […]
Daga Saawuaa Terzunge
Mataimakin shugaban APC shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya ce maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje kamar kashe jam’iyyar ne.
A ranar Laraba ne dai ƙusoshin APC suka tabbatar wa da Aminiya cewa shugaba Tinubu zai damƙa shugabancin jam’iyyar a hannun Ganduje.
Sai dai a sanarwar da ya fitar ranar Alhamis a Abuja, Lukman ya ce bai wa Ganduje shugaban jam’iyyar ya zama “ɗanyen kai.”
Ganduje zai zama shugaban APC na ƙasa
Ban ci bashin N10bn na CCTV ba – Ganduje
Salihu Lukman na cikin waɗanda suka yaƙi Abdullahi Adamu har suka yi nasarar sa shi murabus kafin su kai ga tsige shi.
Amma ya nace maye gurbinsa da Ganduje na nuna rashin damuwa da gwagwarmayar ɗora jam’iyyar kan saiti.
Ya ce, “Wannan zaɓin zai yi watsi da tsarin rabon muƙamai na jam’iyyar wanda da shi aka yi la’akari wurin rabon muƙaman Majalisar Dokoki ta Tarayya.
Ya kuma ce ba shi da matsala da Ganduje a bisa ƙashin kansa amma ba daidai bane a bai wa Arewa maso Yamma shugabancin jam’iyya bayan an bata shugaban Majalisar Wakilai.
Don haka ya nemi a tabbatar da cewa wanda zai shugabanci APC ya fito ne daga Arewa ta Tsakiya domin ci gaba da tabbatar da adalci.