Za a ƙirƙiro ƙarin jiha ɗaya a Nijeriya
Lokpanta da a yanzu ke cikin Jihar Abia, zai kasance babban birnin Jihar Etiti.
Majalisar Wakilai ta gabatar da ƙudurin ƙirƙiro ƙarin jiha guda da za a kira Jihar Etiti a yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya.
Ƙudirin wanda Amobi Godwin Ogah tare da wasu ’yan majalisa huɗu suka gabatar, ya tsallake karatu na farko a majalisar ranar Talata.
- Majalisa ta kori kudurin hana hafsoshin tsaro karkatar da kudade
- An kama shugaban ’yan banga da sassan jikin dan Adam
Ƙudurin na buƙatar yin gyara a sashe na uku na Kundin Tsarin Mulkin ƙasar, domin goge lamba 36 tare da maye gurbinta da lamba 37 don bai wa sabuwar jihar damar shiga jerin jihohin ƙasar, sannan a saka Etiti bayan Enugu cikin jerin sunayen jihohin ƙasar.
Sabuwar jihar wadda za a yanka daga duka jihohin yankin biyar za ta ƙunshi ƙananan hukumomi 11, inda Lokpanta da a yanzu ke cikin Jihar Abia, zai kasance babban birninta.
Ƙananan hukumomin da za su koma sabuwar jihar sun haɗa da Isuikwuato da Umu-Nneochi (Jihar Abia), da Orumba ta Arewa da Orumba ta Kudu (Jihar Anambra), sannan Ivo da Ohaozara (Jihar Ebonyi), sai Aninri da Agwu da Oji River (Jihar Enugu), da kuma Okigwe da Onuimo (Jihar Imo).