Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja
Wannan dai na zuwa ne bayan yadda aka dinga samun matsalolin wutar lantarki a birnin.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya sanar da cewa wasu sassan birnin za su fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na tsawon makonni biyu.
Ɗaukewar wutar lantarki zai fara aiki daga ranar Litinin, 6 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Janairu.
- Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza
- An kashe mutum 9 an jikkata 4 saboda biskit a Jigawa
Sanarwar kamfanin ta bayyana cewa, aikin gyaran layukan wutar lantarki da ke Kukwaba na megawatt 33 da 132 ne zai jawo ɗaukewar wutar.
Yankunan da lamarin zai shafa sun haɗa da Lugbe, Airport Road, Kapwa, NNPC, Games Village, National Stadium, Gudu, Gbazango, Kubwa, Bwari, Jahi, Jabi, Karu, Nyanya, Mararaba da Keffi.
Wannan ɗaukewar lantarki ya biyo bayan wani yanayi na ɗaukewar wutar lantarki da aka fuskanta a baya-bayan nan.