Za a ɗaure tsohon minista shekara 12 a Indonesiya 

An zargi ministan da karkatar da kashi 20 cikin 100 na kasafin kuɗin ma’aikatar.

Za a ɗaure tsohon minista shekara 12 a Indonesiya 

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasar Indonesiya (KPK), ta yi kira da a yi wa Tsohon Ministan Noma, Syahrul Yasin Limpo, ɗaurin shekara 12 kan zarginsa da cin hanci da rashawa.

Limpo kuma zai biya tarar rupiah miliyan 500 (kimanin dalar Amurka 30,600).

A yayin shari’ar da aka gudanar a ranar Juma’a, mai gabatar da ƙara, Meyer Simanjuntak, ya bayyana cewa ana kuma buƙatar Limpo ya biya Rupiah biliyan 44.27 (kimanin dalar Amurka miliyan 2.71) da dalar Amurka 30,000 wanda ake zargin ya karɓa tsakanin 2020 zuwa 2023.

Ana zargin ministan da babban sakatarensa da kuma wani darakta a ma’aikatarsa wajen karɓar waɗannan kuɗaɗe.

Limpo, wanda ya yi aiki a matsayin Ministan Noma daga 2019 zuwa 2023, an zarge shi da karkatar da kashi 20 cikin 100 na kasafin kuɗin ma’aikatar tare da taimaka wa jam’iyyarsa a lokacin babban zaɓen ƙasar.

Simanjuntak, ya ce an samu Limpo da laifin karya dokar yaƙi da cin hanci da rashawa tare da dokar aikata laifuka.