Za a aiko da gawar Oniya Najeriya
Mahukuntan kulob din T-Team na Malesiya sun yanke shawarar aiko da gawar dan Najeriya Dabid Oniya wanda ya mutu a lokacin da yake buga wa kulob din kwallo. dan kwallon ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya samu matsalar bugun zuciya a yayin da kulob din yake wasan sada zumunta da kulob din […]
Mahukuntan kulob din T-Team na Malesiya sun yanke shawarar aiko da gawar dan Najeriya Dabid Oniya wanda ya mutu a lokacin da yake buga wa kulob din kwallo. dan kwallon ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya samu matsalar bugun zuciya a yayin da kulob din yake wasan sada zumunta da kulob din Kelantan a karshen makon jiya. Ana sa ran a aiko da gawar dan kwallon ce kafin karshen wannan mako da muke ciki.
Bayanin haka na kunshe ne a wata sanarwa da wani jami’i na hukumar kwallon kafa ta Malesiya mai suna Datuk Rozi Mannat ya sanar ga kafar sadarwar PM News a ranar Talatar da ta gabata.
“Shirye-shiryen aika wa da gawar Oniya zuwa Najeriya ta kankama, don tuni asibitin Raja Perempuan Zainab II ya kammala shirin yin haka”.
“Za mu tabbatar an aika gawar mamacin gida ba tare da an samu matsala ba, kuma mun yi alkawarin daukar dawainiyar mayar da gawar gida, Najeriya”, inji shi.
Shi dai marigayi Dabid Oniya, dan kimanin shekara 30, shi ne kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta T-Team da ke buga kwallo a rukunin ’yan dagaji a Malesiya. Ya yanke jiki ya fadi ne saboda matsalar bugun zuciya a lokacin da ake wasa. Nan take aka garzaya da shi wani asibiti amma kafin ka ce kwabo rai ya yi halinsa bayan likitoci sun yi kokarin tserar da shi.
A daidai minti na 60 da fara wasa ne aka dakatar da wasan bayan labarin mutuwar Oniya ta isa filin daga asibitin al’amarin da ya sa aka dage kwallo a filin har zuwa wani lokaci.
Jami’an kulob din sun ce sun tuntubi mahaifin Oniya da ke Najeriya da kuma mahaifiyarsa da ke zaune a Uzbekistan a game da gawar dansu, amma mahaifin ya ce a mayar da ita Najeriya don a rufe ta a can.
Al’amarin mutuwar ’yan kwallo a lokacin da ake wasa ba sabon abu ba ne, don kimanin makonni biyu kenan a jere da Aminiya take kawo ratohannin ’yan kwallo da ke mutuwa a yayin da ake kwallo a sassan duniya. Ga shi yanzu an sake kwatawa bayan Oniya ya sake mutuwa a yayin da ake kwallo a Malesiya.