Za a ba da lada ga duk wanda ya fallasa inda za a samu Janar Alkali
Kundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa a shirye take ta ba da lada mai tsoka ga duk wanda ya samu nagartaccen bayanin da zai sa a gano Manjo Janar Muhammad Idris Alkali (mai ritaya) wanda ya bace a watan jiya a Du da ke Jos a Jihar Filato. Mataimakin Daraktan Watsa Labarai na Rundunar Soji […]
Kundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa a shirye take ta ba da lada mai tsoka ga duk wanda ya samu nagartaccen bayanin da zai sa a gano Manjo Janar Muhammad Idris Alkali (mai ritaya) wanda ya bace a watan jiya a Du da ke Jos a Jihar Filato.
Mataimakin Daraktan Watsa Labarai na Rundunar Soji ta Uku da ke Jos, Kanar Kayode Ogunsanya ne ya bayyana haka a wata sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Litinin da ta gabata.
Ya ce, “Rundunar Soji ta Uku ta bukaci mutanen Jihar Filato masu son zaman lafiya, musamman al’ummar yanki Dura-Du da ke Gundumar Du a Karamar Hukumar Jos ta Kudu su ba rundunarmu nagartaccen bayanin da zai sa a gano Janar Alkali (mai ritaya). Za a iya samunmu ta wannan lambar waya kamar haka: 09074028881. Kuma akwai lada mai tsoka ga duk wanda ya ba da bayanin da zai sa a gano Manjo-Janar Alkali.”
Ya ce, ganin sojoji masu yawa a Karamar Hukumar Jos ta Kudu suna gudanar da aikinsu yana da nasaba da yunkurin rundunar sojin don gano Janar Alkali a raye ko a mace.
“Wannan aikin zai sanya mu gano Janar Alkali har ya hadu da iyalinsa idan yana raye, idan kuma ya mutu hakan zai sa Rundunar Sojin Najeriya ta samu damar yi masa jana’izar da ta dace da shi,” inji shi.
Kanar Ogunsanya ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa an samu motoci 11 da gawarwarki biyu daga kududdufin da aka tsamo motar Janar Alkali.
“Har yanzu motoci biyu aka ciro tun bayan da aka ciro motar Janar Alkali,” inji shi.