Za a ba matasa dubu biyar jari a Jihar Kebbi
Jami’in Asusun Rage Radadin Janye Tallafin mai a Jihar Kebbi Alhaji Sama’ila dankasa ya bukaci matasa su rungumi sana’o’in hannu domin dogaro da kai don su taimaka wajen samar wa kansu ci gaba da walwala. Alhaji Sama’ila dankasa, ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da wani shirin samar da aikin yi ga […]
Jami’in Asusun Rage Radadin Janye Tallafin mai a Jihar Kebbi Alhaji Sama’ila dankasa ya bukaci matasa su rungumi sana’o’in hannu domin dogaro da kai don su taimaka wajen samar wa kansu ci gaba da walwala.
Alhaji Sama’ila dankasa, ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da wani shirin samar da aikin yi ga matasa da asusunsa ya kirkiro a Jihar Kebbi.
Alhaji Sama’ila dankasa ya ce an shirya shirin ne domin sama wa matasa aikin yi tare da kawar da rashin aikin yi a tsakanin al’umma, inda ya ce shirin ya kunshi amfani da matasa dubu biyar wadanda za a ba jari da wayoyin salula, domin sayar da katin waya.
Ya ce bayan matasan na farko da za a soma shirin da su, asusun zai kara zakalo wasu matasa domin su amfana a nan gaba. Saboda haka ya yi kira ga matasan da za su amfana da shirin su maida hankali, tare da yin amfani da jarin da za a ba su domin dogaro da kai.
daya daga cikin matasan da suka amfana ga shirin, Malam Umar Abubakar Birnin Kebbi ya gode wa asusun kan kokarin da ya yi wa matasan, tare da yin alkawarin amfani da kayayyakin yadda ya shata.