Za a ba sojan da ya daina shan taba kyautar kudi a Koriya

Ministan Tsaron kasar Koriya ta Kudu ya kaddamar da wani shiri wanda aka yi tanadin ladan kudi ga duk sojan kasar da ya daina shan taba sigari.Kamar yadda fadar yada labarai ta Yonhap ta ruwaito ma’aikatar tsaron za ta bai wa sojan da ya daina shan taba sigari kyautar Dala 3360 (kimanin fiye da Naira […]

Za a ba sojan da ya daina shan taba kyautar kudi a Koriya
Za a ba sojan da ya daina shan taba kyautar kudi a Koriya

Ministan Tsaron kasar Koriya ta Kudu ya kaddamar da wani shiri wanda aka yi tanadin ladan kudi ga duk sojan kasar da ya daina shan taba sigari.
Kamar yadda fadar yada labarai ta Yonhap ta ruwaito ma’aikatar tsaron za ta bai wa sojan da ya daina shan taba sigari kyautar Dala 3360 (kimanin fiye da Naira miliyan daya) da kuma kyautar wasu injinan motsa jiki.
Wani  bincike da ma’aikatar ta yi a shekarar 2015, ya nuna cewa kashi 40 cikin 100 na sojojin kasar suna shan taba. Kuma binciken ya ce dakarun kasar sun fi shan taba bayan shigarsu aikin soja.
Mahukuntar kasar sun ce suna fatan rage yawan masu shan taba da kashi 30 cikin 100 nan da shekarar 2020.
An sanar da shirin ne a ranar Talata (31 ga watan Mayu) wato ranar bikin yaki da shan taba a duniya. Har ila yau, ma’aikatar tsaron kasar ta ce za ta bai wa duk sojan da ya jingine shan taba tallafi wajen kulawa da kiwon lafiyarsa.
Gwamnatin kasar Koriya ta Kudu ta kwashe lokacin mai tsawo tana kokarin ganin ta rage yadda ake yawan shan taba a fadin kasar, ciki har da dokar da majalisar dokokin kasar ta kafa ta kara farashin taba da kashi 80 cikin 100 wadda aka fara aiki da ita a bara.