Za a ba taurarin Kannywood guda 7 lambar yabo a Landan

Wani Kamfanin jarida na birnin Landan mai suna African voice ya zabi taurarin kannywood guda bakwai  domin ba su lambar yabo dangane da  qwazon da suka nuna a masana’antar ta kannywood. Bikin bada lambar yabon za a yishi ne a ranar hudu  ga watan Nuwamba , 2017. Taurarin da zasu amshi lambar yabon sun hada […]

Za a ba taurarin Kannywood guda 7 lambar yabo a Landan

Wani Kamfanin jarida na birnin Landan mai suna African voice ya zabi taurarin kannywood guda bakwai  domin ba su lambar yabo dangane da  qwazon da suka nuna a masana’antar ta kannywood. Bikin bada lambar yabon za a yishi ne a ranar hudu  ga watan Nuwamba , 2017.

Taurarin da zasu amshi lambar yabon sun hada da Nafisa Abdullahi, Hafsat Ahmed, Halima Atete, Ramadan Booth, Sani Ahmad Yaro, Kamal Alkali da Hamisu Lamido Iyantama.

Lambar yabon zai kasance a vangarori uku: ‘yan wasa, bada umarni  da kuma shiryawa.