Za a bai wa kowace jiha tallafin N18bn — Buhari

Kowace jiha za ta biya kudin cikin shekara 30 kan kudin ruwa kashi 9 cikin 100.

Za a bai wa kowace jiha tallafin N18bn — Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da bai wa jihohin kasar 36 tallafin Naira biliyan 656.112 domin cike gibin wasu ayyuka a jihohin.

Bayanan tallafin sun fito ne yayin taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa wanda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta ranar Alhamis.

Wata sanarwa daga ofishin Mataimakin Shugaban Kasar ta ce kowace jiha za ta samu naira biliyan 18.225, wanda za ta biya cikin shekara 30 kan kudin ruwa kashi 9 cikin 100.

A cewar Fadar Shugaban Kasa, an dauki matakin ne saboda a tallafa wa jihohi cimma muradansu na harkokin kudi musamman kasafin kudadensu na shekara.

Wani rahoto da BBC ya wallafa ya ce za a raba kudin ne a mataki shida cikin wata shida kuma ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN) za a rarraba wa jihohin.

Tun a watan Yuli ne Ministar Kudi Zainab Ahmad ta fada wa majalisar cewa za a fara zarar kudi daga asusun jihohin domin fara biyan bashin tallafin farko da aka ba su, amma sai jihohin suka nuna turjiya tare da neman wani agajin, abin da ya sa aka bullo da agajin kasafin kudin kenan.