Za a baiwa maikwarmaton Ikoyi lada, Inji Minista
Ministan Kudi, Kemi Adeosun ta ce a cikin watan nan ne za a saki kudin wanda ya kwarmata yadda aka kai ga gano makuden kudi a wani gida da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas. Ta ce kudin da za a biya shi na daga cikin kudaden da aka riga aka kammala aiki a kansu […]

Ministan Kudi, Kemi Adeosun ta ce a cikin watan nan ne za a saki kudin wanda ya kwarmata yadda aka kai ga gano makuden kudi a wani gida da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas.
Ta ce kudin da za a biya shi na daga cikin kudaden da aka riga aka kammala aiki a kansu a watan Nuwamban da muke ciki.
Aminiya ta ruwaito cewa bayanan da maikwarmaton ya bayar ne ya kai ga gano Dala miliyan 43 da Yuro dubu 27 da 800 daga ginin Hukumar Yaki da Ta’annutin Kudi ke amfani da shi.