Za a bayar da izinin yin rukiyya a asibitocin Saudiyya

Ma’aikatar lafiya ta Saudiyya za ta bai wa masu Rukiya lasisi warkar da marasa lafiya a asibitin masu tabin kwakwalwa, kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, wata jaridar kasar ta ruwaito a ranar Talatar makon jiya.Wata majiya ta bayyana cewa ma’aikatar lafiyar na shirin bayar da izin yin rukiyar ne a wasu zababbun asibitoci. Kuma […]

Za a bayar da izinin yin rukiyya a asibitocin Saudiyya
Za a bayar da izinin yin rukiyya a asibitocin Saudiyya

Ma’aikatar lafiya ta Saudiyya za ta bai wa masu Rukiya lasisi warkar da marasa lafiya a asibitin masu tabin kwakwalwa, kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, wata jaridar kasar ta ruwaito a ranar Talatar makon jiya.
Wata majiya ta bayyana cewa ma’aikatar lafiyar na shirin bayar da izin yin rukiyar ne a wasu zababbun asibitoci. Kuma duk mai bukatar a yi masa addu’ar fitar da aljanni, wato rukya ko rukiya, sai ya aike da neman izini ga sashen shiryarwa da fadakarwa da ke ma’aikatar addinin Musulunci, inda bayan an amince da bukatar za a sanya wa mutum rana da lokaci da wurin yin addu’ar.
Sannan akwai jami’in hukuma da za a turo daga ma’aikatar addinin Musulunci da zai kula da aiki mai rukiyar, ta yadda za tabbbatar ya bi ka’idar Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW). Kuma za a yi rukiyar a kebantaccen wuri, don tabbatar da kariya ga mai addu’ar aljanun da marasa lafiyar.
Majiyar  ta ce, ma’aikatar ba za ta kyale mai rukiya ya kawo dauki a tsarin bayar da magani ko ya nemi bayani game da magungunan da ake bai wa marasa lafiya ba. Idan aka samu mai rukiya ya saba wa kur’ani da hadisi, ko tsarin bayar da magani ga marasa lafiya,jami’in sashen shiryarwa daga ma’aikatar addinin Musulunci zai dakatar da rukiyar, sannan ya bukaci iyalan mara lafiya su nemi wani kwararren mai rukiya da ke da shaidar izinin aikin, kamar yadda majiyar ta bayyana.