Za a bi dokokin kariyar COVID-19 a sansanoninmu —NYSC

NYSC) ta bayar da tabbacin kiyaye dukkan dokokin yaki da annobar COVID-19 da

Za a bi dokokin kariyar COVID-19 a sansanoninmu —NYSC

Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima

Hukumar Kula da Matasa Masu Yi wa Kasa Hidimar (NYSC) ta bayar da tabbacin kiyaye dukkan dokokin yaki da annobar COVID-19 da Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta gindaya a sansanoninta.

Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun daraktanta na watsa labarai da hulda da jama’a, Misis Adenike Adeyemi, ya bayyana ce wa, shugaban hukumar, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim.

Ya ce, hukumar (NYSC) ba ta taba samun rahoton wani daga cikin masu hidimar kasa ya kamu da cutar ba, tun farkon samun rahotan bullar cutur a kasar nan.

Sanarwar ta kara da cewa shugaban ya bayyana hakan yayin wani kwarya-kwaryar taron wayar da kai da aka shirya wa matasa masu hidima ‘yan rukunin ‘B’ a kan cutar da ya gudana a birnin Jos na jihar Filato.

Shugaban ya ce hukumar za ta ci gaba da wayar da kan matasan har sai an fita daga yanayin mayuwacin halin da ake ciki, don samun nasarar gudanar da hidimar kasar cikin nasara.

Shu’aibu ya ce hukumar ta himmatu wajen tabbatar da ba’a samu ko mutum daya daga sansanin masu hidimar kasar ya kamu da annobar Covid-19 ba.

Ya ce, annobar corona sai da ta tilasta rufe rukunin masu hidimar kasa rukuni na daya na 2020 saboda gudun yaduwar annobar a sansanonin masu hidimar kasar.

Hukumar ta ce ta tanadi dukkan kayan kare yaduwar cutar ga masu hidimar kasar a yayin bude sansanin mai zuwa a dukkan fadin kasar nan.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa

Tags