Za a binciki kamfanin jiragen da ya yi amfani da tsani wajen sauko da fasinjoji

Ministan Harkokin  Sufurin Jiragen Sama Sanata Hadi Sirika ya ba da umarnin a binciki kamfanin jiragen saman na Aero Contractors kan amfanin da tsani wajen sauko da fasanjojin da suka shigo jirgin, a karshen makon da ya gabata a filin saukar jiragen sama na Bauchi. Minista Sirika ya ce ya samu rahoton cewa kamfanin ya […]

Za a binciki kamfanin jiragen da ya yi amfani da tsani wajen sauko da fasinjoji
Za a binciki kamfanin jiragen da ya yi amfani da tsani wajen sauko da fasinjoji

Ministan Harkokin  Sufurin Jiragen Sama Sanata Hadi Sirika ya ba da umarnin a binciki kamfanin jiragen saman na Aero Contractors kan amfanin da tsani wajen sauko da fasanjojin da suka shigo jirgin, a karshen makon da ya gabata a filin saukar jiragen sama na Bauchi.

Minista Sirika ya ce ya samu rahoton cewa kamfanin ya yi amfani da tsani wajen sauke fasinjojin da ya dauko, a filin saukar jiragen sama na Bauchi, a ranar Asabar da ta gabata. Ya ce wannan abu da kamfanin ya yi ya saba wa ka’idojin aikin sufurin jiragen sama na Najeriya da  duniya baki daya.
Ya ce wannan bincike da za a yi wa kamfanin, ana son a gano dalilan da suka sanya ya yi amfani da tsanin wajen sauko da fasinjojin da ya dauko, wanda yake da matukar hadari don ganin irin haka ba ta sake faruwa ba, a filayen saukar jiragen sama na kasar nan.
“Hakkin Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya ne ta  tsaya wajen ganin an yi amfani da kayayyakin aikin da ba za su kawo hadari ga fasinjojin da suke shiga jirage a filayen jiragen sama na kasar nan ba. Don haka wannan aika-aika da wannan kamfani ya yi, ba da sanin Hukumar Kula da Filayen Jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ya yi ba,” inji shi.