Za a binciki musababbin mutuwar mage a Pakistan
Kotun birnin Lahore a kasar Pakistan ta yanke wani hukunci bayan da aka kai wani likitan dabboibi kara a gabanta kan kisan mage, inda ta yi marnin binciken musababbin mutuwar kyanwar.Mai kara Atia Masood Chaudhry ta bukaci kotu ta yi rajistar kararta a karkashin sashe na 429 na dokar Penal code, bisa zargin likitan dabbobinta […]
Kotun birnin Lahore a kasar Pakistan ta yanke wani hukunci bayan da aka kai wani likitan dabboibi kara a gabanta kan kisan mage, inda ta yi marnin binciken musababbin mutuwar kyanwar.
Mai kara Atia Masood Chaudhry ta bukaci kotu ta yi rajistar kararta a karkashin sashe na 429 na dokar Penal code, bisa zargin likitan dabbobinta ya kashe mata kyanwa.
Wannan kyanwa da aka yi wa lakabin Moon an binneta a farfajiyar gidan mai ita da ke Karachi. Shi kuwa Mai shari’a Anwarul Hak da yake yanke hukuncin a ranar Talatar da ta gabata, cewa ya yi, lallai a tono kyanwar don gudanar da binciklen musababbin mutuwarta, a karkashin kulawar hukumar shari’a, don tantance musababbin mutuwar, kamar yadda jaridar Dawn ta ruwaito.
Tun cikin watan Mayun wannan shekarar ce mai kara Atia Masood Chaudhry, ta gabatar da kararta, inda ta zargi likitan da ke kula da lafiyar kyanwarta, Owais Anees da yi wa magen kisan gilla.
Masood, wadda Farfesa ce a Jami’ar Punjab, ta ce kyanwarta ’yar wata 18 ta kamu da rashin lafiya a ranar 18 ga Janairun bana, don haka ta biya likitan dabbobi ya zo har gida ya dubata.
Masood ta zargi Anees da karbar mata kudi har Rupees na Pakistan dubu shida a kowane zuwa, amma a wani zuwa na musamman da ya yi sai da ya caje ta kudi har Rupees dubu 25, inda ta ce bayan ta biya shi Rupees dubu 10, sai ya bukaci ta kara masa dubu 15.