Za a binne gawarwaki 60 da ba a gano ’yan uwansu ba a Kaduna
Gwamnatin Jihar Kaduna za ta binne gawarwakin wasu mutane 60 da ba a san masu su ba a makabartar Tudun Wada

Kabarin da aka sanya gawar Marigayiya Maryam Bayero
Gwamnatin Jihar Kaduna za ta binne gawarwakin wasu mutane 60 da ba a san masu su ba.
Sashin Lafiya na Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu zai dauki gawawwakin don binnewa a a Makabartar Layin Bashama da ke unguwar Tudun Wada.
- An rasa yara 2 da gidaje 1,100 a gobarar sansanin gudun hijira a Borno
- Mawaki ya maka BBC Hausa a kotu, yana menan diyyar miliyan 120
Mataimakiyar Sashin lafiya na Karamar Hukumar Kaduna ta kudu- Asmau Saidu Adamu ta sanar cewa za a binne gawarwakin ne a ranar Juma’a 17 ga watan Nuwamba da muke ciki.
“Za a dauko gawarwakin ne daga Asibitin Gwamna Awan zuwa Makabartar Bashama Road, karkashin jagorancin Kwamishinar Lafiya ta Jihar Kaduna, Umma K Ahmed da Shugaban Asibitin Gwamna Awan, Dokta Gebriel Brown,” inji ta.