Za a binne Khamenei a birnin Mashhad
Ɗan Khamenei wato Mojtaba Khamenei na daga cikin waɗanda ake ganin suna kan gaba wajen maye gurbinsa.
Za a binne jagoran addini na Iran, marigayi Ayatollah Ali Khamenei a birnin Masshad kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Fars ya ruwaito a ranar Talata.
Khamenei wanda ya jagoranci ƙasar Iran tsawon shekaru 36, ya yi gamo da ajalinsa bayan wani hari da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a ranar Asabar.
- China ta musanta bai wa Iran tallafin soji
- JIBWIS ta dakatar da tafsirin Sheikh Alƙali Zariya saboda sukar gwamnati
Tun daga yau Laraba ce za a fara gudanar da taron jana’izar Khamenei, a birnin Tehran kamar yadda kafar yaɗa labaran ƙasar ta sanar.
Kafar ta ruwaito cewa za a fara taron da misalin ƙarfe 18:30 na agogon GMT, kuma shirye-shiryen za su gudana na tsawon kwanaki uku kafin a yi jerin gwanon jana’iza.
A yau ɗin ne kuma ake sa ran za a ayyana magajin Khamenei, inda Jaridar NewYork Times ta ambato wasu jami’an Iran na cewa ɗan Khamenei wato Mojtaba Khamenei na daga cikin waɗanda ake ganin suna kan gaba wajen maye gurbinsa.