Za a biya diyyar makabartar Hausawa ta Ibadan – Gwamnati

Gwamnatin Jihar Oyo ta kare kanta a kan zargin cewa za ta kwace makabartar Hausawan Ibadan, inda ta ce, wannan batu ya shafi kauyuka 11 da gonaki da dazuka da ita kanta makabartar kuma yarjejeniya ce aka kulla a tsakanin Gwamnatin Jihar da Gwamnatin Tarayya domin aikin gina tashar ajiye kwantainoni da suka cunkushe a […]

Za a biya diyyar makabartar Hausawa ta Ibadan – Gwamnati

Gwamnatin Jihar Oyo ta kare kanta a kan zargin cewa za ta kwace makabartar Hausawan Ibadan, inda ta ce, wannan batu ya shafi kauyuka 11 da gonaki da dazuka da ita kanta makabartar kuma yarjejeniya ce aka kulla a tsakanin Gwamnatin Jihar da Gwamnatin Tarayya domin aikin gina tashar ajiye kwantainoni da suka cunkushe a tashar jiragen ruwa ta Apapa a Legas.

Gwamnatin ta ce tsohuwar gwamnatin jihar ce ta fara tsara komai shekara biyu da suka wuce inda kuma gwamnatin yanzu ta ci gaba da yarjejeniyar saboda amfaninta ga jama’a.

Kwamishinan Muhalli na Jihar Mista Abiodun Abdulraheem ne ya bayyana  haka lokacin da shugabannin Hausawa a karkashin jagorancin Sardaunan Yamma kuma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin suka gana da shi a ofishinsa a Ibadan. Mista Abiodun Abdulraheem, ya nuna wa shugabannin Hausawan wasu takardu masu dauke da bayanin tsarin karbar makabarta da aka fara a shekarar 2018.

Ya ce, akwai tanadin biyan diyyar makabarta da dukkan filaye da gidaje da gonaki da albarkar da ke cikinsu tare da sama musu wasu wurare na daban.

Da yake yi wa ’yan jarida karin haske bayan ganawar Kwamishinan ya ce, gwamnati ba ta aiki kowa zuwa mika wata wasika mai dauke da batun karbar makabarta ko gidaje da filaye ba. Ya ce, Kamfanin Safiyo na Messers Adeniyi Taiwo and Co. Estate Surbibeyors and Balues wanda ya rika mika wannan takarda ga mutanen da ke zaune a wadannan wurare, aiki yake nema kuma ya yi gaban kansa ne domin gwamnati ba ta aike shi ba.

Bayan kammala ganawar ce lauyan Hausawan Barista Surajo Danbaba, ya yi wa Aminiya bayani cewa, “Ganawar ta ba mu damar gano gaskiyar cewa tun cikin shekarar 2018 tsohuwar gwamnatin jihar ta fara tsara batun karbar wannan makabarta, amma ba mu samu labarin haka ba sai yanzu.”

Kuma mahukunta sun yi ta zaman tattaunawa da mutanen kauyukan da ke zagaye da makabatar, amma ba a taba yin irin wannan zama da shugabanninmu ba, sai yanzu mako hudu da wucewa da muka fara jin rade-radin kwace makabartar. Kuma wani abin mamaki shi ne da farko ma sun nuna cewa, ba su san da wannan magana ba sai da suka ga mun yunkuro domin neman hakkinmu,” inji shi.

Ya ce, “Ai Gwamnatin Jihar ita ce ta mallaki dukkan filaye a cikin huruminta. Gwamnatin Tarayya ba ta da ikon yin wani aiki sai tare da iznin jiha saboda haka wannan batu gaba dayansa mun gano cewa Gwamnatin Jihar Oyo ce take son karbar makabartar daga hannun Hausawa.”

A bayanin da Sardaunan Yamma, kuma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin, ya yi wa Aminiya, ya yi kira da kakkausar murya cewa, “Ya kamata mahukunta su yi adalci a kan wannan matsala. Ya yi tambayar cewa, yaya kuke so mu yi da gawarwakin mutanenmu da ake kawowa kullum daga ciki da wajen jihar ana binne su a wannan makabarta kamar yadda shari’ar Musulunci ta shimfida? Ya kawo misalin yadda wani hadari ya rutsa da mutane a bara inda aka kawo gawarwakin mutum 70 aka haka babban rami aka binne su bayan yi musu jana’iza. Ya sake yin tambayar cewa, yaya kuke so mu yi da tsofaffi da sababbin gawarwakin da kuke son yin amfani da karfinku wajen tone su?”

Binciken Aminiya ya gano cewa, Kwamitin Amintattun Hausawa  suna can suna ci gaba da bibiyar al’amarin makabartar bayan an tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Oyo ce take son karbar makabartar.

Bincike ya tabbatar da cewa, sauran mutanen da ke zaune a kusa da makabartar sun nuna amincewa da biyansu diyyar gonaki da dazukansu kafin a tashe su daga wannan wuri.