…Za a biya wadanda hadarin ya shafa diyyar miliyoyin Naira

A shekaranjiya Laraba ne Sarki Salman na kasar Saudiyya ya bayar da umarnin biyan diyyar Riyal miliyan guda (kimanin naira miliyan 53) ga kowane mutum da ya rasu a hadarin Masallacin Harami ko ya nakasa, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito. Har ila yau, ya ba da umarni biyan wadanda suka samu kananan raunuka […]

…Za a biya wadanda hadarin ya shafa diyyar miliyoyin Naira
…Za a biya wadanda hadarin ya shafa diyyar miliyoyin Naira

A shekaranjiya Laraba ne Sarki Salman na kasar Saudiyya ya bayar da umarnin biyan diyyar Riyal miliyan guda (kimanin naira miliyan 53) ga kowane mutum da ya rasu a hadarin Masallacin Harami ko ya nakasa, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.
Har ila yau, ya ba da umarni biyan wadanda suka samu kananan raunuka diyyar dubu dari biyar na Riyal (kimanin naira miliyan 26). Hakazalika, ya ce mutum biyu daga cikin kowane dangin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin, za su halarci aikin Hajjin badi kyauta bayan an biya su diyyar naira miliyan 53. Sarkin ya yi kuma alkawarin cewa zai karrama dangin mamatan lokacin da suka isa kasar a shekarar 2016.
Bugu da kari, kasar ta dakatar da hulda da kamfanin da ke gudanar da aikace-aikacen fadada masallacin bayan faruwar al’amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 100, ciki har da mahajjatan Najeriya su shida. A ranar Juma’ar da ta gabata ne hadarin ya faru lokacin da wani babban injin gini ya fado kan masallacin sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake shararawa. Hakazalika, an hana manyan jami’an kamfanin fice wa daga kasar har sai bayan kammala bincike.
Kamfanin dai ya shafe shekara hudu yana aikin fadada babban masallacin don samun karin sararin daukar masu ibada da za su kai miliyan biyu a lokaci guda. Wanda idan an kammala zai kai girman kimanin filayen kwalon kafa guda 50.
Za mu tabbatar an biya diyyar – Hukumar Alhazai
A jiya Alhamis, Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya Alhaji Abdullahi Muktar Muhammad ya yi wa sashen Hausa na BBC karin bayani game da yadda za su tabbatar an biya diyyar. “Kamar yadda muka ji a sanarwa ta kafafen yada labarai, Mai girma Sarkin Saudiyya ya yi alkawarin cewa duka wadanda Allah Ya karbi ransu da wadanda suka samu raunuka a cikin wannan hadari za a biya su diyya, amma hanyoyin da za a bi a karbi diyyar ba a ba mu su a rubuce ba daga hukumomin Saudiyya,” inji shi. Daga nan an tambaye shi: Kamar daga bangarenku wane matakai ne za ku bi daki-daki har ku kai ga tantance wadanda suka samu wannan diyyar da kuma hanyar da za a tabbatar da cewa ta kai gares u? sai ya ce,“Na farko dai wadanda suka rasu an riga an san su, wadanda suka ji rauni ma an riga an san su. Kuma an san jihohin da suka fito, an san iyalansu. To za mu bi ta hanyoyin hukumomin alhazan jihohin da suka yi musu rijista don tabbatar da cewa an bi wannan alkawari da Sarkin Saudiyya ya yi kuma ya kai ga magada yadda yakamata.
Kuma tattare da haka a jiya wakilanmu da suke birnin Makkah sun yi zama da hukumonin alhazan wadannan jihohi na Kaduna da Katsina da Gombe da kuma wasu daga cikin dangin wadanda suka rasu, wadanda suka samu zuwa aikin hajjin. Mun sanar da su wannan sanarwa da muka samu. Abin da yanzu muke saurare shi ne mu samu takarda rubutacciya daga ma’aikata, ko ofishi, ko hukumar da za a fuskanta domin tabbatar da cewa an karbi wannan diyyar an mika ta gare su.
Kuma idan an dawo gida hukumar alhazai ta kasa za ta sanya ido ta tabbatar da cewa magadan wadannan bayin Allah da suka rasu hakkin nan ya kai gare su. Su kuma wadanda suka samu rauni tun da suna nan a nan Saudiyya idan har kafin a kammala aikin hajji ne gwamnatin Saudiyya ta cika wannan alkawari, za a tabbatar da cewa sakon ya isa gare su. Kuma idan ya isa gares u za mu sanar da duniya cewa wannan sakon ya isa ga wadanda yakamata.”