Za a biya ’yan majalisa masu barin gado biliyan 30 a matsayin ‘kudin sallama’
Kudaden dai za a raba wa Sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai
Hukumar Gudanarwar Majalisar Dokoki ta Kasa ta fara shirin biyan Sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai masu barin gado kudaden sallama da suka kai Naira biliyan 30.
Akawun majalisar, Yahaya Danzariya, ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
- Majalisar Dokokin Filato ta kori dukkan Ciyamomin Jihar
- Ba za mu yi zanga-zanga kan cire tallafin mai ba – ’Yan kwadago
Majalisar Dokokin Najeriya ta tara dai wacce aka rantsar ranar 11 ga watan Yunin 2019 ana sa ran kawo karshenta ranar 13 ga watan Yuni, ranar da za a rantsar da sababbi.
Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya karanta takardar ga mambobin majalisar yayin zamansu na ranar Laraba.
A cewar wasikar, Danzariya ya ce, “dukkan ’yan majalisar za su karbu takardar tantancewa domin a biya su kudaden sallamar daga ofishin Akawun majalisar sannan su mayar da shi bayan sun cike a ofis mai lamba 2.154 ko kuma 2.031, a sashen kudi kafin ranar 9 ga watan Yunin 2023.”
An dai ware sama da Naira biliyan 30 ga majalisar ta tara mai barin gado da kuma na maraba ga sababbin ’yan majalisa da hadimansu a kasafin kudi na 2023.
A karkashin kasafin dai, majalisun sun ware Naira 194,839,144,401 a bana,
A wani labarin kuma, an ware sama da Naira biliyan daya ga shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnati, yayin da za a kashe wa tsofaffin Shugabannin Kasa da Mataimakansu Naira biliyan 2.3.
Daga cikin wadanda za su amfana da wannan garabasar akwai tsofaffin Shugabannin Kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari da Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar da Yakubu Gowon; sai kuma Mataimakan Shugaban Kasa Atiku Abubakar da Namadi Sambo.
Alkaluma dai na nuna cewa za a kashe kimanin Naira biliyan 64.72 domin sallamar masu rike da mukaman siyasa da Shugaban Kasa da Mataimakinsa da Gwamnoni da hadimansu da Ministoci da Kwamishinoni da ’yan majalisun tarayya.