Za a biya ’yan Najeriya miliyan 70 tallafin N75,000 don rage talauci
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta biya ’yan Najeriya dubu saba’in Naira 75,000 kowannensu domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa.
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta biya ’yan Najeriya dubu saba’in Naira 75,000 kowannensu domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa.
Babban Hadimin Shugaban Ƙasa Kan Harkokin Jama’a, Aliyu Audu ya sanar cewa matakin ya dace da tsarin Gwamnatin Shugaba Tinubu na rage talauci a tsakanin ’yan Najeriya.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jagorantar taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC ya bayyana cewa ’yan Najeriya shaida ne a kan nagartattun ayyukan Shugaba Tinubu a watanni 19 da ya yi a bisa mulki.
A cewarsa, ƙwararan matakan da Gwamnatin Tinubu ta ɗauka sun haifar da kyawawan sakamako ga iyalai da ɗaiɗaikun ’yan Najeriya a cikin gida da ƙasashen waje, tare jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje.
- Yadda aka yi jana’izar mutane 86 bayan fashewar tankar mai a Dikko Junction
- NAJERIYA A YAU: Yadda Rashin Ɗaukar Darasi Ya Haddasa Gagarumin Asara A Suleja
Ya bayyana cewa a shekara ɗaya ’yan kasuwa daga ƙasashen waje sun zuba jari Dala 7.69 a Najeriya, sakamakon kyawawan tsare-tsaren da Babban Banki Najeriya (CBN) da Gwmanatin Tarayya suka ɓullo da su.
Ya ƙara da cewa gwmanatin tana yin duk mai yiwuwa wajen rage basukan da ake bin Najeriya a kasashen waje, domin dawo da martabar kasar.
Ya ci gaba da cewa yawan ɗanyen man da Najeriya ke haƙowa ya ƙaru wanda a dalilinsa kuɗaɗen da jihohi da ƙananan hukumomi ke samu daga asusun tarayya ya ninki sau uku a cikin shekara guda, inda suke iya sauke nauyin da rataya a wuyansu na yi wa al’umma ayyuka.
A cewarsa, tsaro ya inganta a mulkin Tinubu a yayin da ake samun ƙaruwar amfanin gona.
An kuma samu karin kuɗaɗen shiga daga ɓangarorin da ba na man fetur ba.