Za a buɗe makarantu 23 da aka rufe tsawon shekaru 10 a Oyo

Za mu ɗora wa shugabannin kananan hukumomin laifi muddin aka sake samun wata tangarda.

Za a buɗe makarantu 23 da aka rufe tsawon shekaru 10 a Oyo

Gwamnatin Jihar Oyo ta bayar da umarnin a hanzarta bude Makarantun Sakandare 23 da aka rufe shekaru 10 da suka gabata a dalilin rikicin kan-iyaka a tsakanin Kananan Hukumomin Atiba da Afijio.

Mataimakin Gwamna Barista Bayo Lawal ne ya bayar da wannan umarni a ranar Alhamis a wajen taron masu ruwa da tsaki da aka yi a Zauren Taro na Western Hall da ke Sakatariyar Gwamnati a Ibadan.

Ya nemi Shugabannin Kananan Hukumomin biyu da su tabbatar da samar da tsaro da zaman lafiya a yankunan nasu domin kuwa za a dora alhaki a kansu muddin aka sake samun wata baraka a nan gaba a yankin.

Mataimakin Gwamnan wanda yake riƙe da shugabancin hukumar kula da sasanta rikicin kan-iyaka a jihar, ya roƙi ’yan Majalisar Dokokin masu wakiltar kananan hukumomin da su yi duk mai yiwuwa wajen haɗa kai da shugabannin al’umma domin tabbatar da samun nasarar buɗe makarantun.

Ya miƙa irin wannan roƙon ga dattawan yankin da su kalli irin matsalar da rikicin kan-iyakar ya haifar ta fannin gurbacewar karatun yara a yankin.

Barista Bayo Lawal ya tabbatar da cewa Ma’aikatar Ilimi ce ke da alhakin sanya ido wajen ganin an buɗe makarantun tare da komawar yara cikin azuzuwa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Kwamishinan Ilmi Farfesa Salihu Adelabu da shugaban hukumar samar da ilmi na bai-daya, Dakta Nureni Aderemi Adeniran da sarakunan gargajiya na yankin na daga cikin mahalarta taron.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja