Za a bude makarantu ranar 15 ga watan nan
Gwamnatin Tarayya ta canja shawara kan rufe makarantun firamare da sakandare zuwa 13 ga Oktoba, sakamakon cutar Ebola, inda ta ce za a koma makaranta a tsakiyar wannan watan, watau ranar 15 ga wata. A karshen watan jiya ne gwamnatin ta kara hutun makarantar saboda tsoron yaduwar cutar Ebola, sai dai a shekaranjiya Laraba, Ministan Lafiya […]
Gwamnatin Tarayya ta canja shawara kan rufe makarantun firamare da sakandare zuwa 13 ga Oktoba, sakamakon cutar Ebola, inda ta ce za a koma makaranta a tsakiyar wannan watan, watau ranar 15 ga wata.
A karshen watan jiya ne gwamnatin ta kara hutun makarantar saboda tsoron yaduwar cutar Ebola, sai dai a shekaranjiya Laraba, Ministan Lafiya Dokta Onyebuchi Chukwu ya shaida wa manema labarai a fadar Shugaban kasa cewa, Majalisar Zartarwa ta kasa ta yanke shawarar a sake bude makarantun a tsakiya Satumba bisa shawarar kwararru da kuma nasarar dakile cutar.
Ya ce majalisar ta umarci Ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau ya kira taron gaggawa da daukacin kwamishinonin ilimi na jihohi domin su cim ma matsaya kan ranar da za a koma makarantun.
Minista Chukwu ya ce a yanzun haka akwai mutum 296 da ake sanya ido a kansu a kasar nan kan cutar, ciki har da mutum 255 a Fatakwal da kuma 41 a Legas.
Minsitan ya ce ana ci gaba da jinyar mutum biyu da suka kamu da cikakkiyar cutar Ebola a kasar nan, matar likitan nan na Fatakwal Samuel Amenou da ’yar uwarsa, wadanda dukkansu biyu suna kebe a wasu cibiyoyin killace masu cutar a Legas da Fatakwal.
Ya ce jimillar wadanda aka tabbatar Ebola ta kama su ne mutum 18, inda aka samu 14 a Legas sai hudu a Fatakwal, kuma an magance na mutum takwas an sallame su daga asibiti, yayin da bakwai suka mutu.
Dokta Chukwu wanda ya musanta rahotannin da ke cewa, wadanda suka harbu da Ebola 60 sun bace a Fatakwal, ya ce binciken kwakwaf da aka gudanar kan jita-jitar bayyanar cutar a Abuja da Kalaba ya gano akasin haka.
Ya ce ana jiran sakamakon gwajin da aka gudanar kan dalibin nazarin shari’a na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya don tabbatar ko ya kamu da cutar Ebola ko a’a.
Ministan ya ce, gwamnati na duba yiwuwar daukar mataki kan ma’aikacin ECOWAS, Mista Olu-Ibukun Koye da ya kai kwayar cutar Ebola Fatakwal. Ya ce, a yanzu bai dauke da kwayar cutar a cikin jininsa don haka ba zai iya harbar wasu da it aba. To amma za su tuntubi Ma’aikatar Harkokin Waje ta ba su shawara, kuma za su duba dokokin kasar nan don yi musu ganin tsofaffin dokoki ne game da kebe jama’a, don yi musu gyara su tafi da kalubalen zamani.