Za a bude masallacin mata zalla a Ingila

A makon jiya ne wata kungiyar mata Musulmi da ke kasar Birtaniya ta sanar da aniyyarta ta gina masallacin mata zalla a birnin Canterbury da ke Ingila. kungiyar ta ce za ta yi hakan ne domin bai wa mata damar taka muhimmiyar rawa a addini, ciki har da ba su damar wajen jagorantar sallar Juma’a […]

Za a bude masallacin mata zalla a Ingila
Za a bude masallacin mata zalla a Ingila

A makon jiya ne wata kungiyar mata Musulmi da ke kasar Birtaniya ta sanar da aniyyarta ta gina masallacin mata zalla a birnin Canterbury da ke Ingila.

kungiyar ta ce za ta yi hakan ne domin bai wa mata damar taka muhimmiyar rawa a addini, ciki har da ba su damar wajen jagorantar sallar Juma’a da ba su horo domin zama limamai. Shugabar mata Musulmi da ke birnin Bradford, Bana Goma ta bayyana wa jaridar The Telegraph cewa: “Masallatai ba sa kulawa da mata irin yadda ya kamata kuma wannan ya sa madadin mu yi ta korafi, ya dace mu dauki wani mataki a kan hakan. Amma nan da ’yan kwanaki za mu yi karin bayani ciki har da kudin da za a kashe wajen aikin,” inji ta.
Kodayake, lokacin da aka tambaye ta yawan mambobin kungiyarsu ta bayyana cewa akalla sun kai dubbai.
Akwai akalla Musulmi da suka kai miliyan biyu da dubu 800 a kasar Birtaniya, adadin da ya fi kashi hudu cikin 100 na al’ummar kasar.
Amma ba wannan ne karon farko da aka fara bude masallacin mata zalla ba. Domin a watan Fabrairun bana, an taba yin hakan a birnin Los Angeles na kasar Amurka, inda aka bai wa mata zalla da kananan yara ’yan kasa da shekara 12 damar yin sallar Juma’a da kansu sau daya a kowane wata. Hakazalika, kimanin shekara biyar da suka wuce, an taba samun wata mace ’yar kasar Kanada mai suna, Raheel Raza, wanda ta jagoranci maza da mata a lokaci guda sallar Juma’a a wani karamin masallaci da ke birnin Odford na kasar Birtaniya.
Har ila yau, manyan mazhabobi uku cikin hudu na Sunni sun yarda mace za ta iya jagorantar mata ’yan uwanta sallah. Kodayake, yawancin malaman fikihu sun ce ba ya halarta mace ta jagoranci maza da mata . Amma mata kamarsu Raheel da Bana suna kalubatantar hakan, inda suka dage kan cewa babu wurin da aka ce a Al-kur’ani an haramta wa mata jan sallah.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa