Za a bude masallacin mata zalla a Ingila (2)
Alkawari babban al’amari ne a rayuwarmu ta yau da kullum. Haka kuma cika alkawari na daya daga cikin mumimman dabi’u da addini ke kira a yi shi. Duk mutumin da ya zamanto mai cika alkawari, babu shakka zai kasance mutum mai mutunci a idanun jama’a, haka kuma zai kasance mai martaba da kima a rayuwarsa. […]
Alkawari babban al’amari ne a rayuwarmu ta yau da kullum. Haka kuma cika alkawari na daya daga cikin mumimman dabi’u da addini ke kira a yi shi. Duk mutumin da ya zamanto mai cika alkawari, babu shakka zai kasance mutum mai mutunci a idanun jama’a, haka kuma zai kasance mai martaba da kima a rayuwarsa. A wannan zamani namu, mun shantake, mun siffantu da halayyar rashin cika alkawari. Har ma mun sanya wa al’amrin suna ‘African Time’ wanda haka ke nuna cewa ba mu daraja lokaci ko alkawari. Domin jaddada muhimmancin cika alkawari, sha’irinmu na yau, Malam Nasiru G. ’Yan Awaki ya zayyana wannan wake. A nazarci waken da kaifin basira, domin fa’idantuwa:
Daga Nasiru G. Ahmad ’Yan Awaki
Sunanka farko ya Allah,
Tsira amincinka Allah,
kara su gun Manzon Allah,
Shi munka burin mui kalla,
Ko da cikinsa mafarkinmu.
Yau damuwa ce ke raina,
Bisa batu da muke raina,
Cikin darenmu ko rana,
Son rai gare mu abin kauna,
Kan dukkanin harkokinmu.
Cika shi alkawari sunna,
Ga dukka manya da kanana,
Saba shi ko aikin barna,
Da Rabbi sarki ya yi hana,
Ga duk maza har matanmu.
Muna barin sa umarnin nan,
Na Rabbana da ya yo din nan,
Ayar cikin kur’anin nan,
“Ku zam cika alkawarin nan,
Don za a tambayi shi” gun mu.
“Ya muminai shin mis sa ne,
Kuke batu” a tsaye zaune,
“Da ba ku yin sa a aiki ne?”
Fadin Ta’ala sarki ne,
Gare mu kan hali namu.
Abin takaici mun kyale,
Wannan umarni sai hole,
Ran tambaya ba ma kalle,
Halinmu ba kyawu walle,
Don babu alkawari gunmu.
Alkawari in mun dauka,
Na lokaci kan duk harka,
Ko yin wani aiki gun ka,
Ni kam gaske nake dauka,
Amma cikawa bai samu.
Murna muke in mun saba,
Muna ganin ai mun caba,
Har jinjina muka zam karba,
Kuka ya dace mui sharba,
Don ya kazanta aikinmu.
Ga ‘yan siyasa ko ado ne,
Suna ganin mai sauki ne,
Hanyar zuwa ga muradi ne,
Bayan guba mai halaka ne,
Gare su har umma tamu.
Babu dalilin sabawa,
Sai don mugunta aikawa,
Nuna isa ko burgewa,
Ko sakaci ga mutuntawa,
Da munka yi bisa zatinmu.
karfe goma ka ce zan zo,
Ko ko ka ce wa wane ya zo,
Ba kai shiri goman ta zo,
Sai uzuri ba yin kwazo,
Ba ka nadama ko damu.
Ka ce wa yaro bar kuka,
Abu kaza ne zan ba ka,
Alkawari ne ka dauka,
Amma ka saba wa danka,
Ka muna tarbiyyar danmu.
Wannan fa mugun hali ne,
Amma gare mu abin so ne,
Da takamar mun burge ne,
Bayan ko laifi babba ne,
Za ai hisabinsa kanmu.
Bai zam cikar addini ba,
Bai zam shi halin kirki ba,
Bai zam abin tunkaho ba,
Bai zam cika ga kamala ba,
Saba wa alkawari namu.
In ka tsananta ga cikawa,
Ka kyamaci a yi sabawa,
Wai ka yi halin Turawa,
Halinka na da tsanantawa,
Don ka ki mugun halinmu.
Fada a cika dattaku ne,
Ko da ko mai yin yaro ne,
Ko a ina mai kima ne,
Abin a ba wa aminci ne,
Mai martaba gun sarkinmu.
Da mu ya dace ai koyi.
Ya zam gare mu abin yayi,
A zahiri da cikin rayi,
Mun bar Nasara kadai ke yi,
Mun zabi daukar son ranmu.
Wannan abin jin kunya ne,
Gare mu babban aibu ne,
Abin ragewar kima ne,
Da za mu taru mu gaggane,
Da sun yi kyau harkokinmu.
Tsari rashin sa ka damun mu,
Na lokutan harkokinmu,
Loto abin banza gunmu,
Shi ne ko ai rayo tamu,
In ya wuce bai komen mu.
Fada a saba laifi ne,
Loto a sauya aibu ne,
Warware zance nakasa ne,
kin cika kawari sabo ne,
Mu zam cire shi a halinmu.
Shi alkawar ai kaya ne,
Bisa ga kai nannauya ne,
Kula da shi imani ne,
Cika shi aikin lada ne,
Mai nauyaya mizaninmu.
Allah Ya ba mu dukan dace,
Mu’amalarmu ta zam tsafce,
Ta zam gudana dinance,
Yara su koya su gwanance,
Su zam du’a’i bayanmu.
Nan zan tsaya na ciyo burki,
Tabara ba mu yawan dauki,
Mu tabbata a halin kirki,
Kullum bisa dukka mataki,
Na rayuwa har karshenmu.
Mai tsara wakar Nasir ne,
G. Ahmad rarrauna ne,
Gare mu mai yin addu’a ne,
Bisa ga kyautata hali ne,
A dukka alkawarorinmu.