Za a buga wasan kusa da na karshe na Gasar Cin Kofin Zakarun Kulob-Kulob Na Turai

A ranar Talata 22 da Laraba 23 ga wannan wata da muke ciki ne ake sa ran za a fafata a gasar zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da  UEFA Champions League matakin kusa da na karshe watau Semi-Fainal.kungiyoyin kwallon kafa hudu ne suka kai wannan mataki.  A ranar Talatar ce kungiyar kwallon […]

Za a buga wasan kusa da na karshe na Gasar Cin Kofin Zakarun Kulob-Kulob Na Turai

Micheal PatiniA ranar Talata 22 da Laraba 23 ga wannan wata da muke ciki ne ake sa ran za a fafata a gasar zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da  UEFA Champions League matakin kusa da na karshe watau Semi-Fainal.
kungiyoyin kwallon kafa hudu ne suka kai wannan mataki.  A ranar Talatar ce kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ke Sifen za ta kece raini da Bayern Munich da ke Jamus yayin da a washegari 23 ga wata kuma za a yi wasa a tsakanin kulob din Atletico Madrid da ke Sifen da kuma na Chelsea da ke Ingila.
Ana sa ran za a yi wasa zagaye na biyu ne a ranakun Talata 29 da kuma Laraba 30 ga wannan wata da muke ciki kuma daga nan ne za a tantance kungiyoyin kwallon kafa biyu da za su buga wasan karshe a watan Mayu mai zuwa.