‘Za a ci gaba da ba wa manoma rancen kudi’

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce za a ci gaba ba wa manoma rance, ganin yadda ‘yan Najeriya ke rungumar harkar noma suke kuma cin amfana. A jawabinsa ga ‘yan Najeria a Ranar Damokradiyya, Buhari ya ce gwamnati za ta farfado da harkar noman auduga da masaku ta hanyan bayar da basuka. A cewarsa Babban […]

‘Za a ci gaba da ba wa manoma rancen kudi’

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce za a ci gaba ba wa manoma rance, ganin yadda ‘yan Najeriya ke rungumar harkar noma suke kuma cin amfana.

A jawabinsa ga ‘yan Najeria a Ranar Damokradiyya, Buhari ya ce gwamnati za ta farfado da harkar noman auduga da masaku ta hanyan bayar da basuka.

A cewarsa Babban Bankin Najeriya (CBN) zai bayar da basukan ne domin saukaka noma da samar da auduga da kuma shigo da injinan masaku daga ketare.

Kazalika za a ci gaba da samar da ingantaccen takin zamani mai arha, wanda yanzu akwai masana’antunsa 31 a kasar, wadanda kuma ke samar da ayyuka ga ‘yan kasa.

A cewarsa gwamnati na yin iya kokarinta don samar da hanyoyin kauyuka domin saukaka wa manoma fitar da amfanin gona daga yankunansu zuwa manyan tituna da kasuwanni.