Za a ci gaba da gasar zakarun kulob na Turai

A ranar Talata mai zuwa watau 16 ga watan Fabarairun 2016 ne ake sa ran za a ci gaba da fafatawa a gasar zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da UEFA Champions League.Idan ba a manta ba tun a watan Disamban 2015 ne aka tafi hutu bayan an kammala zagayen farko na gasar. […]

Za a ci gaba da gasar zakarun kulob na Turai
Za a ci gaba da gasar zakarun kulob na Turai

A ranar Talata mai zuwa watau 16 ga watan Fabarairun 2016 ne ake sa ran za a ci gaba da fafatawa a gasar zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da UEFA Champions League.
Idan ba a manta ba tun a watan Disamban 2015 ne aka tafi hutu bayan an kammala zagayen farko na gasar. Yanzu za a shiga zagaye na biyu ne inda kungiyoyin kwallon kafa 16 suka kai wannan mataki.
kungiyoyin kwallon kafar da za su fafata a ranar Talatar sun hada da Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa wacce za ta hadu da ta Chelsea da ke Ingila sai wasa na biyu da za a kara tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Benfica da ke Portugal da kuma ta Zenith Saint Petersburg da ke Rasha.
A washegari ne kuma watau ranar Laraba 17 ga watan Fabrairun 2016 za a kece raini a tsakanin kulob din KAA Gent na Beljiyam da Wolsfurg na Jamus sai wasa na biyu a tsakanin AS Roma na Italiya da kuma Real Madrid na Sifen.
Amma sai a makon gobe sauran kungiyoyin kwallon kafa guda takwas za su yi nasu wasan da suka hada da FC Barcelona da Arsenal da Bayern Munich da Jubentus da sauransu.
Ba a taba samun kungiyar da ta lashe gasar sau biyu a jere ba tun bayan da aka sake wa gasar fasali a shekarar 1990.
A bara kulob din FC Barcalona ne ya lashe gasar bayan ya lallasa kulob din Jubentus a wasan karshe da ci 3-1.  Idan Barcelona ta sake lashe kofin a bana, zai kasance ta kafa sabon tarihi a gasar.  Yanzu dai lokaci ne kawai zai nuna ko hakan zai iya faruwa ko a’a.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa