Za a ci gaba da rufe iyakar Najeriya da Benin

Shugaban hukumar shige da  ficen kayayyaki na kasa (kwastam), Alhaji Abdullahi Dikko Inde ya ce hukumar ba za ta bari a rika shigo da kayayyaki daga  bakin iyakar Najeriya da  jamhuriyar Benin ba, har sai jami’an kwastam na kasar  ta Benin sun mutunta yarjejeniyar kasa-da-kasa da aka shinfida.Shugaban ya ce bai yiwuwa  a ce kasashen […]

Za a ci gaba da rufe iyakar Najeriya da Benin

Shugaban hukumar shige da  ficen kayayyaki na kasa (kwastam), Alhaji Abdullahi Dikko Inde ya ce hukumar ba za ta bari a rika shigo da kayayyaki daga  bakin iyakar Najeriya da  jamhuriyar Benin ba, har sai jami’an kwastam na kasar  ta Benin sun mutunta yarjejeniyar kasa-da-kasa da aka shinfida.
Shugaban ya ce bai yiwuwa  a ce kasashen biyu su cimma matsaya a kan  dokokin junansu,  amma sai  jami’an kasar ta  jamhuriyar  Benin su koma daga  gefe  suna yin yadda  suka ga dama.
Ya ce ya kai  wannan batun  gaban shugaban Najeriya  da  ministar kudi kuma ya bayyana musu irin yadda jami’an kasar ta  jamhuriyar  Benin suke  wasa  da  yarjejeniyar da aka cimma, wanda idan ta kama a  rufe  bakin iyakar, sai a rufe.
Shugaban kwastan din yana magana ne sa’ilin da yake  ganawa  da  masu fiton kayayyaki da ke Jihar Legas, yayin da  suke  kokawa  domin ganin an bude bakin iyakar Najeriya da jamhuriyar  Benin har na tsawon watanni biyu kuma  hakan ya kawo  musu  cikas  wajen neman abin zaman gari.
Da aka tambaye shi ko yana sane da jami’ansa masu kwace kayan mutane ko bayan sun biya kudin ka’ida  na fito, sai Alhaji Dikko Inde ya ce duk jami’in kwastam din da aka kama yana karbe kayan mutane, bayan an biya kudin ka’ida na  fito, ya kuka da  kansa, domin za a kore shi daga aiki, idan kuma an samu har ya karbi kudi, sai an gurfanar da shi  gaban alkali  kafin a kore bakin aikin.
Alhaji Dikko Inde ya ce hukumar  kwastan ta samar da tsarin aiki mai kyau, wanda ya ba ma’aikata dukkan hakkokinsu  tare  da inganta  muhallinsu  da duk wani abu  da ka iya kyautata aikinsu, don haka ba su da kowace irin hujja ta karbar hanci da rashawa. yace  samar da aikin su cikin sauki yasa  hakan ya kara samar da kudin shiga  ga hukumar ta kwastan.
Da kuma yake  bayanin sabon tsarin aikinsu ta amfani da na’ura  mai kwakwalwa, sai ya ce kayan da za ka jira  cikin sati ko fiye, yanzu cikin awoyi 54, ka karbi kayanka kuma  daga yanzu ba za a iya yin fasa kwabri ta hanyar shigowa da kayayyakin da ba a amince da su ba, sabanin yadda ake yi a da.
Alhaji Dikko Inde ya ce kafin ka shigo da kaya, sai an nuna  maka an yarda a shigo da su ko a’a.
Daga karshe ya bayyana jin dadinsa na yadda  hukumar ta yi nasarar karbar aikinta na karbar haraji  daga hannun wasu kafanionin kasashen  waje,  wadanda  suka  dade suna tatsar  Najeriya kuma tana biyan su kudin aiki  ko sun karba yadda  ya dace ko kuma akasi  aka samu.  “Najeriya na da wadatattu kuma gogaggun ma’aikatan kwastan da suka san wannan aikin, amma kuma sai aka dauka aka danka wa  wasu kamfanonin kasashen  waje”. Inji shi.