Za a ci gaba da rufe masallatai da majami’u a Lagos

Masallatai da coci-coci da sauran wuraren ibada za su ci gaba da kasancewa a rufe a jihar Legas. Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Legas Anofiu Elegushi ne ya bayyana haka ranar Talata a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai. Mista Elegushi ya ce ba zai yiwu a bude masallatai da coci-coci a […]

Za a ci gaba da rufe masallatai da majami’u a Lagos

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu tare da Maidakinsa a lokacin da suke ibadar Ista a gida

Masallatai da coci-coci da sauran wuraren ibada za su ci gaba da kasancewa a rufe a jihar Legas.

Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Legas Anofiu Elegushi ne ya bayyana haka ranar Talata a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai.

Mista Elegushi ya ce ba zai yiwu a bude masallatai da coci-coci a wannan lokaci ba a jihar  duba da yawan karuwar masu cutar coronavirus, da kuma kasancewar Legas cibiyar annobar.

“Tun kafin umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar, mun yi zama da shugabannin addini da ma’aikatar lafiya ta Legas, mun tattauna yiwuwar bude wuraren ibada.

“A taron da muka yi mun cimma matsaya cewa babu yiwuwar bude wuraren ibada a yanzu.

“Limamai da fada-fada sun shaida mana ba su da ikon tabbatar da cewa mutum 20 ko 50 ne kawai za su iya yin taron ibada a masallatai ko coci-coci.

“Kamar yadda wani limami ya fada, ba shi da ikon takaita yawan mutanen da za su bi shi sallah, domin idan ya yi gaba yana ba da sallah bai san me ke wanzuwa a bayansa ba.

“Don haka ba za mu bude wuraren ibada a yanzu ba, har sai an cimma yarjejeniyar bin ka’idar kariya, duk da gwamnatin tarayya ta ce a bude wuraren ibada, hakan ba zai hana jihohin daukar matakan da za su kare kan su ba”

A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta ba da sanarwar bude masallatai da coci-coci a fadin kasar, inda ta bayyana sassauta dokar kulle da ta ayyana domin yaki da cutar coronavirus.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara