‘Za a ci gaba da samun matsala idan kananan hukumomi ba su samu ’yanci ba’

Sakataren karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato, Alhaji Shehu Bala Usman ya ce za a ci gaba da samun matsaloli a kasar nan matukar kananan hukumomi ba su samu ’yancin samun kudinsu daga Asusun Tarayya ba.Alhaji Shehu Bala Usman ya ce matukar kudin kananan hukumomin ba sa zuwa asusunsu kai- tsaye daga […]

‘Za a ci gaba da samun matsala idan kananan hukumomi ba su samu ’yanci ba’
‘Za a ci gaba da samun matsala idan kananan hukumomi ba su samu ’yanci ba’

Sakataren karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato, Alhaji Shehu Bala Usman ya ce za a ci gaba da samun matsaloli a kasar nan matukar kananan hukumomi ba su samu ’yancin samun kudinsu daga Asusun Tarayya ba.
Alhaji Shehu Bala Usman ya ce matukar kudin kananan hukumomin ba sa zuwa asusunsu kai- tsaye daga Gwamnatin Tarayya za a ci gaba da fama da matsalar talauci da rashin aikin a tsakanin jama’a “Domin misali idan aka turo wa karamar hukuma kamar Naira miliyan 100 a wata, da zarar gwamnatin jiha ta zabtare wasu kudin daga karamar hukuma sai a ga a karshe karamar hukumar ta rasa abin da za ta biya albashin ma’aikatanta, balle ta samu kudin da za ta
yi ayyukan raya kasa. Babu idan kananan hukumomin suna samun kudinsu daga Asusun Tarayya kai-tsaye, za su rika yin ayyukan raya kasa da za su taimaki al’ummar yankunan karkara,” inji shi.
Sakataren, ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammad Buhari da ’yan Majalisar Dokoki ta kasa da takwarorinsu na jihohi, su yi wani abu kan wannan matsala ta ’yancin kananan hukumomi. Domin ganin sun samu damar da za su rika yi wa al’ummarsu na yankunan karkara.
Da ya juya ga irin nasarorin da suka samu a karamar Hukumar Jos ta Arewa, Alhaji Shehu Bala ya ce daga lokacin da suka zo zuwa yanzu sun samu nasarar hada kan al’ummar karamar Hukumar Jos.
Ya ce “Mun ziyarci dukkan mazabun karamar hukumar guda 20 muka shaida wa mutanenmu cewa mu hada kai don mu samu zaman lafiya da ci gaba a karamar hukumar. Wadannan kiraye- kiraye da muka yi ta yi wa al’ummarmu kan muhimmancin zaman lafiya da hada kai, sun yi matukar tasiri, domin a yanzu mun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a karamar hukumar.
Ya ce sun tsara ayyukan raya kasa da dama, suna jiran kudi ne kawai, don su gudanar da su.
Ya yaba wa Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong kan yadda yake tafiya da kowa a jihar, inda ya ce gwamnatin Lalong ta nuna cewa gwamnati ce ta kowa da kowa.