Za a ci gaba da shari’a ba sai Ganduje ya halarci zaman kotu ba — Alƙali
Gwamnatin Kano ta ce ta tanadi shaidu 15 da za su bayyana a gaban kotu.
Babbar Kotun Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta ba da umarnin ci gaba da sauraron shari’ar da ake tuhumar tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ba tare da ya halarci zaman kotun ba.
Wannan na zuwa ne bayan kotun ta ƙi amincewa da roƙon da masu ƙara suka yi na neman kotun ta ba da umarnin kama tsohon gwamnan bisa ƙin halartar zaman kotun da ya gudana a yau Alhamis.
- Auren jinsi ya haramta a Burkina Faso
- Chuchu: Kotu ta hana a gwada ƙwaƙwalar matar da ta kashe yaron gidanta
Tun da farko Lauyoyin Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Adeola Adedipe (SAN) suka nemi kotu da ta sa a kama Ganduje bisa ƙin halartar zaman kotun da ya yi bayan kotun ta ba shi sammaci ta hanyar bugawa a jarida.
Sai dai kotun ta amince da buƙatar masu ƙara da suka nemi ta ɗauki waɗanda ake ƙara a matsayin sun musanta laifin da ake zargin su da shi don haka za ta ci gaba da shari’ar.
Ana iya tunawa cewa, Gwamnatin Kano ce ta yi ƙarar tsohon gwamnan gaban kotu bisa tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da zargin karɓar cin hanci, karkatar da kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma da kadarorin gwamnati.
Waɗanda ake karar tare da tsohon gwamnan sun haɗa da matarsa Hafsat Umar da wasu mutane da suka haɗa Abubakar Bawuro da Umar Abdullahi Umar da Jibrilla Muhammad da Kamfanin Lamash Properties Ltd da Kamfanin Safari Textiles Ltd da kuma Kamfanin Lesage General Enterprises.
Gwamnatin Kano ta ce ta tanadi shaidu 15 da za su bayyana a gaban kotu.
Sai dai Barista Nuraini Jimoh wanda shi ne lauyan masu kariya, ya soki roƙon masu gabatar da ƙara, inda ya kafa hujja da cewa bai kamata a saurari roƙon ba duba da cewa akwai roƙo guda biyu da suke da shi da suka hayda da sukar hurumin kotu da kuma wani rokyon da suke da shi a gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara.
Aminiya ta ruwaito cewa kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 23 da 24 ga Oktoba 2024 don sauraron sukar da Ganduje ya yi a gaban kotu tare da ci gaba da sauraron shari’ar.