Ba za a samu karancin Fetur a Kano ba —Dillalai Mai

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) reshen Jihar Kano, ta ba da tabbacin samar da isasasshen mai a jihar, duk da matsalar safara da aka samu sakamakon zanga-zangar #EndSARS a Najeriya. Shugaban reshen, Alhaji Bashir Danmalam ne ya bayyana wa manema labarai hakan, duba da matsalar karancin man fetur da wasu jihohi ke fuskanta, […]

Ba za a samu karancin Fetur a Kano ba —Dillalai Mai

Yadda karancin Man Fetur ke haddasa cunkosun ababen hawa.

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) reshen Jihar Kano, ta ba da tabbacin samar da isasasshen mai a jihar, duk da matsalar safara da aka samu sakamakon zanga-zangar #EndSARS a Najeriya.

Shugaban reshen, Alhaji Bashir Danmalam ne ya bayyana wa manema labarai hakan, duba da matsalar karancin man fetur da wasu jihohi ke fuskanta, ciki har da Birnin Tarayya Abuja, inda matsalar ta fi kamari.

Ya ce babu bukatar mutane su damu domin kungiyar ta yi tsare-tsaren samar da wadataccen man fetur ga jihohin da ke shiyyar da suka hada da Kano, Katsina, Bauchi, Yobe da Jigawa.

Alhaji Bashir Danmalam ya yaba wa Daraktan Gudanarwar Man Fetur na Kasa,  Lawal Musa da ya ba da damar ci gaba da rarraba man fetur a fadin Najeriya bayan cikas da zanga-zangar #EndSARS ta haifar.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa